Waken suya zai sa yaranku su kara tsayi; in ji kwararriya a kimiyyar abinci

Waken suya zai sa yaranku su kara tsayi; in ji kwararriya a kimiyyar abinci

- Farfesa Ibiyemi Olayiwola, kwararriya a bangaren kimiyyar abinci, ta gabatar da takarda a kan muhimmancin waken suya

- Olayiwola ta ce waken suya yana da matukar taisiri wajen magance matsalar karancin kuzari a jikin yara

- Kazalika, ta shawarci iyaye mata su ciyar da yaransu waken suya domin tabbatar da sun girma sosai

Wata kwararriya a bangaren kimiyyar abinci mai gina jiki, Farfesa Ibiyemi Olayiwola, ya shawarci iyaye mata su ciyar da yaransu waken suya da ababen da aka sarrafa daga waken suya don su tabbatar yaransu sun girma sosai.

A cewarta cin waken suya zai taimakawa yara wajen samun garkuwa daga rashin kuzari da cututtuka da suka danganci rashin kuzarin waɗanda ka iya haddasa ƙarancin tunani, kamar yadda Tribune ta rawaito.

Olayiwola, farfesa a jami'ar tarayya ta Noma da ke Abeokuta, Jihar Ogun, ta bayyana hakan ne yayin da ta ke magana akan "Waken suya don ceto kuzari" a taron ƙalubalen ƙarancin abinci mai gina jiki a Najeriya karo na bakwai.

KARANTA: Siyasar Kano: An yi hannun riga tsakanin Ganduje da Sha'aban Sharada

Ta bayyana cewa waken suya na ɗaya daga cikin abinci da yara ke buƙatar su ci don su ƙara tsayi saboda yana ɗauke da sinadaran gina jiki masu tarin yawa kuma jiki na sarrafa sinadaran cikin sauƙi.

Waken suya zai sa yaranku su kara tsayi; in ji kwararriya a kimiyyar abinci
Waken suya zai sa yaranku su kara tsayi; in ji kwararriya a kimiyyar abinci
Source: Original

Acewarta, fiye da kaso 30% na waken suya sinadarin gina jiki ne, kuma ya fi nama sinadaran kuzari. Yana ƙunshe da kitse mai kyau, kuma babu sinadarin Kwalestaral.

Ana iya yin awara, madarar wake da sauransu wanda zai yiwa dukkan shekaru daɗin ci da sha.

Ƙwararriyar masaniyar abincin ta ce babu wanda ya tsira daga ƙaranchin sinadarin gina jiki, amma, yara, iyaye masu shayarwa, da mata masu ciki sun fi haɗarin kamuwa da rashin kuzari sakamakon rashin samun abinci mai gina jiki.

KARANTA: FG: CBN za ta fara rabawa masu kiwon kaji da tsuntsaye tallafin biliyan N12.55

Farfesa Olayiwola ta bayyana cewa a shekaru 20 da suka gabata, ba'a samu wani cigaba na azo a gani ba wajen magance matsalar rashin kuzari a tsakanin yara ƴan ƙasa da shekara biyar da kuma mata masu juna biyu ba.

Sun ƙara da cewa kaso 25% cikin yara masu ƙasa da shekara 5 ne suke samun mafi ƙarancin abin da ake buƙata na abinci mai gina jiki wanda ya haɗar da shuke shuke.

Ta ƙara da cewa "mu na tsammanin iyaye mata su baiwa yaransu dukkan na'ukan abinci kala biyar da jiki ke bukata wanda ya haɗar da ganyenyayyaki da kayan marmari. Iya kaso 11% ne suke iya bin wannan tsarin, kuma hakan matsala ce gagaruma."

A ranar Laraba ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa ministar kudi ,Zainab Ahmed, ta sanar da cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da bude iyakokin kan tudu guda hudu.

Iyakokin guda hudu da za'a bude sune kamar haka: Illela a Jihar Sokoto, Maigatari a jihar Jigawa, dukkansu a arewacin Nigeria.

Sai kuma iyakar Seme da ke Jihar Legas, yankin kudu maso yamma, da iyakar Mfun da ke yankin kudu maso kudu.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel