Jerin yan kwallo 10 mafi yawan albashi a duniya na shekarar 2020

Jerin yan kwallo 10 mafi yawan albashi a duniya na shekarar 2020

- Cristiano Ronaldo ya zo na biyu a lambar yabon gwarzon dan kwallon shekara na FIFA

- Dan kwallon kasar Poland da Bayern Munich, Robert Lewandoski, ya doke shi wannan karon

- Amma Ronaldo ya doke dukka sauran yan kwallon duniya wajen yawan albashi

Dan kwallon kungiyar Arsenal, Mesut Ozil, duk da halin tsaka mai wuyan da yake ciki ya shiga jerin yan kwallo mafi yawan albashi a duniya na shekarar 2020.

An cireshi daga cikin jerin masu bugawa kungiyarsa Arsenal wasa wannan kakan karkashin koci, Mikel Arteta.

Amma duk da haka ya fi Paul Pogba na Manchester United daukan albashi.

Amma dan kwallon Juventus, Cristiano Ronaldo, ya zarce dukkan yan kwallon duniya inda yake dauka £88.5 million a shekara.

Ya wuce abokin hamayyarsa, Lionel Messi wanda yake daukan £83.4m da £2.4 million.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya koma Abuja bayan mako daya a Daura

Jerin yan kwallo 10 mafi yawan albashi a duniya na shekarar 2020
Jerin yan kwallo 10 mafi yawan albashi a duniya na shekarar 2020
Asali: Depositphotos

Ga jerin yan kwallo mafi yawan albashi na 2020 (Forbes)

1. Cristiano Ronaldo (Juventus) - £85.8m

2. Lionel Messi (Barcelona) - £83.4m

3. Neymar (Paris Saint-Germain) - £76.6m

4. Mohamed Salah (Liverpool) - £28.2m

5. Kylian Mbappe (Paris Saint-Germain) - £27.1m

6. Andres Iniesta (Vissel Kobe) - £23.7m

7. Mesut Ozil (Arsenal) - £23m

8. Paul Pogba (Manchester United) - £22.8m

9. Oscar (Shanghai SIPG) - £22m

10. Antoine Griezmann (Barcelona) - £21.4m

A bangare guda, an fito da jerin ‘yan wasan kwallon kafan da ba a taba yin irinsu ba. France Football ce tayi wannan aiki da taimakon wasu kwararrun ‘yan jarida 140.

Jaridar The Sun ta ce an zabi rukunin ‘yan wasa 11 har kashi uku. Irinsu Cristiano Ronaldo da Lionel Messi suna cikin sahun farko na jerin taurarin.

Rahoton ya tabbatar da cewa tsofaffin ‘yan wasa Pele da marigayi Diego Maradona sun samu shiga wannan sahu, amma babu wurin Zinedine Zidane.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng