Shugaba Buhari ya koma Abuja bayan mako daya a Daura

Shugaba Buhari ya koma Abuja bayan mako daya a Daura

Shugaba Muhammadu Buhari ya koma birnin tarayya abuja bayan mako daya da yayi mahaifarsa, Daura, a jihar Katsina.

Buhari ya tafi Daura daga Abuja makon da ya gabata.

Shugaba Muhammadu Buhari ya koma Abuja ne bayan ganawa da daliban makarantar sakandaren gwamnati na kimiyya, dake garin Kankara, jihar Katsina.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi maraba da sakin daliban makarantar GGSS Kankara a jihar Katsina, mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki.

Buhari ya siffanta cetonsu a matsayin babban sauki ga iyayensu, kasar, da kuma duniya gaba daya.

Shugaba Buhari ya koma Abuja bayan mako daya a Daura
Shugaba Buhari ya koma Abuja bayan mako daya a Daura
Source: Twitter

KU KARANTA: Bayan garkuwa da mutane 35, yan Boko Haram sun kai hari Mafa

A bangare guda, kungiyar Miyetti Allah MACBAN ta karyata cewa ta shiga cikin tattaunawa da yan bindiga wajen sakin daliban makarantar sakandare gwamnatin GGSS Kankara, a jihar Katsina.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, a ranar Laraba, ya ce gwamnatin ta tuntubi Miyetti Allah domin tattaunawa da yan bindiga kan sakin dalibai da aka sace a makarantarsu.

Sakataren kungiyar Miyetti Allah na kasa, Baba Othman Ngelzarma, ya bayyanawa Saturday Sun a hirar wayan tarho cewa bai da masaniya kan abinda Masari ke magana a kai.

DUBA: Yan Boko Haram sun yi garkuwa da fasinjoji 35 a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel