Barkewar korona karo na 2: Sama da mutum 1,000 sun sake harbuwa
- Cutar korona tana cigaba da barkewar a Najeriya a karo na biyu inda sabbin mutum 1145 suka kamu a ranar Alhamis
- Jihohin da ke kan gaba a yawan masu cutar a ranar Alhamis sun hada da Legas, Abuja da jihar Kaduna
- An samu mutum daya da ya riga mu gidan gaskiya a ranar Alhamis yayin da aka sallama 335 daga asibiti
Bayan a kalla watanni tara da fara samun cutar korona a Najeriya, Najeriya ta samu sama da mutum 1,000 da suka harbu da muguwar cutar a rana daya.
Hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta sanar da harbuwar sabbin mutum 1,1145 a cikin jihohi 23 na kasar a ranar 17 ga watan Disamban 2020.
An fara samun mai cutar korona a kasar nan a ranar 27 ga watan Fabrairun 2020.
Legas ce jihar da ke kan gaba a ranar Alhamis yayin da sabbin mutum 459 suka harbu da cutar a jihar. Babban birnin tarayya na Abuja yana da sabbin mutum 175 yayin da Kaduna ta samu mutum 138 dauke da cutar duk a rana daya.
KU KARANTA: Kotun daukaka kara ta soke hukuncin Olisah Metuh, ta bukaci sake shari'a
Da wannan yawan jama'an ne kasar Najeriya ke da sama da mutum 76,000 da suka kamu da muguwar cutar tun bayan barkewarta.
A yayin da kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar korona ya sanar da cewa kasar na fuskantar barkewar cutar a karo na biyu, yawan masu cutar na ranar Alhamis ya bayyana hakan.
An gano cewa wani mutum daya ya rasu sakamakon cutar a ranar Alhamis, hakan yasa yawan wadanda cutar ta kashe a Najeriya ya kai 1,201.
Amma kuma, an sallama mutum 335 daga asibiti bayan gwagwarmaya da muguwar cutar da suka yi a ranar Alhamis. Hakan yasa yawan wadanda suka warke daga cutar ya kai 67,110.
KU KARANTA: 2023: Yarima ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin kasa
A wani labari na daban, wani dan majalisar wakilai, Sam Onuigbo ya bar jam'iyyar PDP zuwa jam'iyya mai mulki ta APC, Premium Times ta wallafa.
Dan majalisar, mai wakiltar mazabar Ikwuano/Umuahia da ke jihar Abia, ya bayyana canja shekarsa ta wata wasika wacce kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila, ya karanta a ranar Alhamis.
Kamar yadda aka saba, shugaban marasa rinjaye, Ndudi Elumelu ya bayyana rashin amincewarsa dangane da canja shekar Onuigbo, inda ya bukaci kakakin ya kwace kujerar, bukatar da bata samu karbuwa ba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng