Gwamnan Sokoto Tambuwal ya killace kansa, yana jirar sakamakon gwajin korona

Gwamnan Sokoto Tambuwal ya killace kansa, yana jirar sakamakon gwajin korona

- Aminu Waziri Tambuwal, gwamnan jihar Sokoto ya killace kansa yayin da ya ke jiran sakamakon gwajin korona

- Gwamnan ya sanar da cewa wasu mutane da ya yi cudanya da su yayin tafiye-tafiyen aiki sun kamu da cutar don haka zai killace kansa don a masa gwaji

- Gwamnan ya umurci mataimakinsa, Manir Muhammad Dan'Iya ya cigaba da jagorancin jihar har zuwa lokacin da zai san matsayinsa

Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya ce ya killace kansa sakamakon mu'amalla da ya yi da wasu mutane wadanda daga baya aka gano sun kamu da cutar korona wato COVID 19.

Gwamman ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a mai dauke da saka hannun sa, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan Sokoto Tambuwal ya killace kansa, yana jirar sakamakon gwajin korona
Gwamnan Sokoto Tambuwal ya killace kansa, yana jirar sakamakon gwajin korona. Hoto daga @daily_trust
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Hotunan auren kotun matashin Kano da matarsa Ba'Amurkiya

Sanarwar ta ce, "Sakamakon tafiye tafiyen aiki da na yi 'yan kwanakin da suka gabata, inda na yi cudanya da wasu mutane wadanda daga baya an gano sun kamu da korona, likitoci sun shawarce ni da in killace kai na.

"Don haka, zan dakatar da aiki da kuma cudanya da mutane na tsawon lokacin da likitoci suka umurta daga ranar Juma'a 18 ga watan Disamba," in ji shi.

Gwamnan ya umurci mataimakinsa, Hon. Manir Muhammad Dan'Iya (Walin Sokoto) ta karbi ragamar jagorancin jihar kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ta tanada.

KU KARANTA: Mun binciko gwamnan Arewa da ke da hannu a ta'addanci a yankin, in ji APC

Tambuwal ya bukaci mutanen Jihar su cigaba da bin dokokin kiyayye kansu da hukumomin lafiya suka bada na bada tazara, saka takunkumin rufe fuska, wanke hannu da sauransu don dakile yaduwar cutar.

"Ina bukatar addu'o'in ku a kamar yadda na saba musamman a wannan lokacin. Allah ya albarkaci al'ummar Jihar Sokoto da Najeriya baki daya," gwamnan ya kara da cewa.

A baya kunji wasu miyagu da ake zargin yan bindiga ne sun tare tawagar Manjo Sanusi Muhammad Asha, Sarkin Kauran Namoda a Jihar Zamfara inda suka kashe mutum takwas ciki har da yan sanda guda uku.

SaharaReporters ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a babban titin Gusau zuwa Funtua.

Majiyoyi sun ce sarkin yana kan hanyarsa zuwa hallarton wani taro ne a Gusau yayin da yan bindigan suka afka wa tawagarsa suka kashe yan sanda guda uku.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel