Hotunan auren kotun matashin Kano da matarsa Ba'Amurkiya

Hotunan auren kotun matashin Kano da matarsa Ba'Amurkiya

- Wani mutum mai shekara 23 dan asalin jihar Kano, Suleiman Isah, ya auri wata yar Amurka, Janine Anne Reimann, an daura auren a kotu

- Hotunan bikin ya nuna yan uwa da abokai don ganin irin salon soyayyarsu

- Matar tayi shiga irin ta gargajiya don yin dai dai da al'adar mijin ta

Soyayya babu ruwanta da shekaru. Wani mutum dan asalin jihar Kano, Suleiman Isah ya tabbatar da hakan ta hanyar auren Janine Anne Reimann mai shekaru 46.

Idan za a iya tunawa matar tazo Najeriya don ta auri burin zuciyar ta kwanakin da suka gabata kamar yadda Hotuna suka dinga zagaye kafar sadarwa, tare da hada zazzafar muhawara.

DUAB WANNAN: Yan bindiga sun kai wa tawagar sarakin Kauran Namoda hari, mutum takwas sun mutu

An daura auren su ranar Lahadi, 13 ga Disamba a gaban yan uwa da abokai a Gasau Panshekara da ke jihar Kano.

Ranar Alhamis, 17 ga Disamba, ma'auratan sun sake karfafa alaka ta hanyar yin aure a wata kotu da ke jihar.

A cewar wata majiya, an yi bikin a hukumar adana bayanai a Kano. Hotunan bikin sun nuna ma'auratan cikin shigar gargajiya inda matar ta daura zanin ankara.

KU KARANTA: Hotonun Buratai da maciji a gonarsa ya janyo cece-kuce bayan ya yi muƙus a game da sace daliban Kankara

Angon kuma ya saka babbar riga da hula yayin da suka rike takardar shaidar auren su a gaban allon hukumar.

Wasu hotunan kuma mutane sun zagaye ma'auratan.

Kalli hotunan bikin a kasa:

Hotunan auren kotun matashin Kano da matarsa Ba'Amurkiya
Hotunan auren kotun matashin Kano da matarsa Ba'Amurkiya
Asali: Facebook

A bayan kunji cewa, Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya bayyana yadda ya saka baki aka dawo da ɗaliban makarantar sakandare ta Ƙanƙara 344 ba tare da biyan kuɗin fansa ba.

A ranar Juma'a da ta gabata ne aka sace yaran daga makarantar su da ke garin Kankara.

Duk da cewa Boko Haram ta yi ikirarin cewa itace ta sace yara 524, gwamnatin Katsina ta ce ɗalibai 344 kawai aka yi garkuwa da su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel