Sau daya suka bamu abinci cikin kwanaki 2, inda muke barci muke bahaya: Daya daga cikin yaran Kankara
- Gwamnatin jihar Katsina ta karbi bakuncin daliban GGSS Kankara da safiyar Juma'a
- An dawo da yaran Katsina daga dajin Zamfara inda aka boyesu
- Sun bayyana abubuwan da ya faru da su a kwanaki shida da sukayi cikin daji
Daliban makarantar Kankara da aka sako daren Alhamis, sun bayyana halin da suka shiga a hannun yan bindigan da suka yi awon gaba da su mako daya yanzu.
Yayin magana da Channels TV da safiyar nan bayan gwamnan jihar, Aminu Masari, ya karbi bakuncinsu a gidan gwamnatin jihar dake Katsina.
"Sau daya muka ci abinci cikin kwana biyu," daya daga cikin yaran ya fada.
Ya kara da cewa yanzu haka ba shi da lafiya, kuma sun sha matukar wahala cikin daji.
Wani yaron cikin daliban ya bayyana cewa a inda suke kwana suke fitsari da bahaya.
KU KARANTA: Mun bi umurnin Buhari, mun bude iyakoki: Hukumar shiga da fice
Mun kawo muku cewa daliban GSSS Kankara na jihar Katsina da 'yan bindiga suka sace sun iso gidan gwamnati.
Jami'an tsaro ne suka yi musu iso har cikin gidan gwamnatin jihar Katsina.
A ranar Alhamis, 17 ga wata aka sako daliban makarantar sakandaren kimiya dake Kankara akalla 340 yanzu.
Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da haka.
DUBA NAN: Shugaba Buhari zai hadu da daliban Kankara 344 da aka sako
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya sanar da hakan a hirarsa da wani dan jaridan Aljazeera, Ahmed Idris.
"Kawo yanzu, an bamu dalibai 340, daga baya an kara da 4, yanzu akwai dalibai 344 dake hanyarsu ta zuwa Katsina yanzu," Masari ya bayyana.
A ranar Juma'a 11 ga wata ne 'yan bindiga suka afka GSSS Kankara da ke jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da daruruwan dalibai makarantar, bayan isar Shugaba Muhammadu Buhari Daura, garinsa na haihuwa da sa'o'i kadan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng