Utomobong: Yadda aka kama kasurgumin dan fashi da ya kashe kwamishinan 'yan sanda

Utomobong: Yadda aka kama kasurgumin dan fashi da ya kashe kwamishinan 'yan sanda

- Mashahurin dan fashi Kingsley Utomobong ya shiga hannu bayan kisan mataimakin kwamishinan yan sanda a jihar Cross River

- Mataimakin Kwamishinan ya gamu da ajalinsa bayan da motar da yake ciki ta lalace kuma ya kira matarsa don tazo ta dauke

- Wata majiya ta bayyana cewa Kingsley da tawagarsa sun dade suna barna, sai dai kusancinsa da gwamna Ben Ayade ya hana a dauki mataki akan sa

Mashahurin shugaban yan fashi a Jihar Cross River, Kingsley Utomobong, da tawagar sa sun shiga komar yan sanda bayan kisan mataimakin kwamishinan yan sanda, Egbe Edum.

Yan bindiga sun harbe Edum ranar Laraba, 2 ga Disamba, a yankin mil 8, kan titin Murtala Mohammed a Calabar, SaharaReporters ta ruwaito.

An ruwaito cewa an kai masa hari ne lokacin da yake jiran matar sa bayan motar da yake ciki ta lalace.

Utomobong: Yadda aka kama kasurgumin dan fashi da ya kashe kwamishinan 'yan sanda
Utomobong: Yadda aka kama kasurgumin dan fashi da ya kashe kwamishinan 'yan sanda. Hoto: @SaharaReporters
Source: Twitter

Wata majiyar yan sanda ta shaidawa SaharaReporters an samu kayayyakin marigayi Edum a wajen Utomobong da tawagarsa.

DUBA WANNAN: Hotonun Buratai da maciji a gonarsa ya janyo cece-kuce bayan ya yi muƙus a game da sace daliban Kankara

Utomobong, wanda ya shahara wajen ayyukan fashi a fadin jihar, ana ganin kusancin sa da Ben Ayade, gwamnan jihar ne ya hana a dauki mataki akan shi.

Ya shahara a wajen jami'an tsaro a fadin jihar. Ana zargin shi ya kashe Ebenezer Ika a watan Afrilu 2018.

Majiyar ta ce, Utomobong da tawagar sa ba su san cewa Edum dan sanda bane kuma dan uwan mataimakin gwamna.

Majiyar ta ce, "an samu kayayyakin mutumin a wajen Kinsley da tawagar sa. Ba su san cewa dan sanda bane ko dan uwan mataimakin gwamna," a cewar majiyar.

"Mataimakin Kwamishinan yana tafiya zuwa Calabar kuma har sun zama abokai da wani lauya a motar haya. Ba wanda ya san dan sanda har suka isa Calabar kuma motar da suke ta lalace a babban titin Calabar.

"Ya kira matar sa ya fada mata inda ya ke da tazo ta dauke shi. Ban san mai yasa ya ware daga inda sauran fasinjoji suke ba ko kuma mai yasa bai dauko bindiga ba a matsayin sa na jami'in tsaro lokacin da ya bar cikin mutane.

KU KARANTA: An kama Bishop na coci yana lalata da matar wani faston da ke ƙarƙashinsa

"Sai ya matsa gaba shi da abokin sa lauya, anan mutanen Kinsley suka tare su. Aka nemi su bada jakun jakun nan su. Lauyan ya bayar, amma ACP yaki bada tasa jakar. Sai suka harbe shi a hannu don ya saki jakar. Ya dinga zubar da jini har ya mutu.

"Da matar sa tazo taga yana zubar da jini, ta gigice ta fada kwata da motar cikin firgici. Sai bayan ya mutu aka samu bayanin cewa mahaifiyarsa kanwar mataimakin gwamna ce.

"Kingsley ya dade yana ta'addanci ba a daukar mataki har sai da yayi wa na gida. Kaga yadda gwamnati ke daukar mataki in abu ya shafe su?"

Yan sanda suna tuhumar Umotobong. Idan za a iya tunawa a watan Fabarairu, Utomobong ya bayyana a wani bidiyo yana saran wani Eloka Nwankwo da adda.

A wani labarin, gwamnatin tarayyar Najeriya, a ranar Lahadi ta ce shirin samar da ayyuka na musamman, SPW, guda 774,000 zai fara ne a ranar 5 ga watan Janairun shekarar 2021.

Karamin ministan Kwadago da samar da ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ne ya shaidawa The Nation hakan ranar Lahadi a Abuja.

Shirin samar da ayyukan ga masu sana'o'in hannu na watanni uku inda za a rika biyansu N20,000 duk wata ya samu tsaiko sakamakon rashin jituwa tsakanin ministan da tsohon shugaban hukumar samar da ayyuka ta kasa, NDE, Nasir Ladan da Buhari ya sallama daga aiki makon data gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel