Yadda 'yan sanda suka dinga yi wa mutumin da aka sace wa mota dariya
- Tun bayan dakatar da 'yan Sandan SARS, 'yan fashi suka yawaita musamman a jihar Uyo
- Wani mutum ya bayyana yadda 'yan fashi suka kwace masa mota kuma ya nemi taimakon 'yan sanda
- A cewarsa, bayan ya rokesu, sai suka bushe masa da dariya, suka ce tunda sun sa an dakatar da SARS, kadan ya gani
Wani mutum wanda 'yan fashi suka kwace wa mota ya ce ya nemi taimakon 'yan sanda amma sun zolaye shi da cewa tunda har 'yan Najeriya suka bukaci a kawo karshen SARS, dole ne su fuskanci kalubale.
SARS wasu 'yan sanda ne wadanda suka addabi al'umma kafin sifeta janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu ya rushe su.
Wasu 'yan Najeriya sun koka a kafafen sada zumuntar zamani a kan rashin tsaron da ya addabi kasa a lokacin.
Premium Times ta ruwaito yadda wani mutum mai suna Cardinal Usanga, ya bayyana yadda ta kaya dashi a coci a jihar Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.
KU KARANTA: Satar 'yan makaranta: Wasu daliban na cigaba da bullowa daga daji, Mai ba Gwamna shawara
Yace an ga motarsa kirar Toyota Camry, bayan 'yan fashin sun barta a wani wuri a garin.
Kamar yadda yace: "Yan fashin sun yi yunkurin harbi na, sai suka fitar dani daga motata. Bayan sun wuce da motar tawa, sai na hango wata motar 'yan sanda, na tsayar dasu na sanar musu ina bukatar su taimaka min su kwato min motata.
"Sai 'yan sandan suka ce, 'wannan ne ake kira EndSARS'. Suka sheke da dariya suka wuce. "
Bayan dakatar da 'yan sandan SARS, an samu 'yan fashi a kalla guda 40 a cikin garin Uyo kadai.
An kai korafi ga gwamna Udom Emmanuel a kan matsalar rashin tsaro da ke addabar jihar. A ranar Alhamis, 10 ga watan Disamba, gwamnan ya bayar da motocin sintiri 30 ga jami'an tsaro don su taimaka wurin kai dauki a kan harkar tsaron jihar.
KU KARANTA: Satar 'yan makarantan Kankara: Babu gwamnati a kasar nan, Ezekwesili
A wani labari na daban, iyayen daliban GSSS Kankara da ke jihar Katsina, wadanda aka sace sun taru sun yi makil a harabar makarantar suna jiran komawar yaransu kamar yadda gwamnati tayi musu alkawari.
Sun taru ne bayan 'yan kwanaki kadan da faruwar lamarin, wanda satar yaran ya girgiza kowa a kasar nan.
Iyayen suna ta zaman jiran ganin dawowar yaransu. Yayin da 2 daga cikin iyayen suke tattaunawa da gidan talabijin din Channels, sun ce sun kasa barci. Sun kara da bayyana yadda za su cigaba da zama a makarantar har ranar da yaransu zasu koma garesu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng