Ortom ya bukaci matasan jiharsa da su kare kansu da yankunansu

Ortom ya bukaci matasan jiharsa da su kare kansu da yankunansu

- 'Yan bindiga sun kaiwa kauyen Agboughuo, wanda yake wajen garin Makurdi, hari da misalin karfe 11pm

- Sanadiyyar harin, sun kashe wani fasto, matarsa, tsohon makaho, sannan sun kashe yaran tsohon guda 2

- Bayan nan ne gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya shawarci matasa da su yi kokarin kare kansu da kansu

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya shawarci matasan jiharsa da su yaki 'yan ta'adda da 'yan fashi kada su tsaya jiran hukuma.

Gwamnan ya bayar da wannan shawarar ne bayan wasu 'yan ta'adda sun afka wa kauyen Agboughul da ke wajen Makurdi da misalin karfe 11pm, inda suka kashe wani lauya, Moses Udam, wanda fasto ne a Gospel Faith Mission, matarsa Nkechi da wani tsohon makaho, Mazugu Nyikor, mai shekaru 88.

An tsinci gawar mata da mijin, sannan sun ji wa yaran Nyikor 2, ciwo da alburusai, sannan sun tsere da kanwar faston, inda suka bukaci N200,000 a matsayin kudin fansa.

Ortom ya bukaci matasan jiharsa da su kare kansu da yankunansu
Ortom ya bukaci matasan jiharsa da su kare kansu da yankunansu. Hoto daga @Vangaurdngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Satar 'yan makaranta: Wasu daliban na cigaba da bullowa daga daji, Mai ba Gwamna shawara

Vanguard ta ruwaito yadda 'yan bindigan, wadanda ake zargin makiyaya ne suka yi wa faston yankan rago sannan suka harbi matarsa.

Sai dai bayan sun harbi daya daga cikin 'ya'yan makahon, daya ya tsere ya sanar da jama'a halin da ake ciki.

Jami'an OPWS, NSCDC da wasu jami'an tsaron jihar Benue sun isa kauyen ranar Talata da daddare, sannan kuma sun yi alkawarin tsare kauyen.

Bayan Gwamna Samuel Ortom ya kai wa kauyen ziyara, cikin takaici da alhinin faruwar lamarin ya shawarcesu da kada su kuskura su daga wa 'yan ta'addan kafa.

KU KARANTA: Kankara: Iyayen dalibai sun jeru a farfajiyar makaranta suna jiran dawowar 'ya'yansu

A cewar gwamnan, "Mun yi tunanin shiga siyasa zai taimaki yankinmu, amma bamu yi tunanin za a kashe mana mutane ba. Muna yin iyakar kokarinmu na ganin mun samar da tsaro yadda ya kamata, amma ba zai yuwu a ce kowacce anguwa ko kauye suna da jami'an tsaro ba.

"Yan bindiga musamman makiyaya, wadanda ba 'yan Najeriya ba, suna cigaba da samu cikin tashin hankali da damuwa, don haka wajibi ne matasa su dage wurin tsare kansu da kansu. Musamman saboda yaranmu da al'umarmu."

A wani labari na daban, bayan Dino Melaye ya baiwa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan hakuri, akan yadda ya tsaya kai-da-fata wurin ganin sun saukeshi daga mulki, Bala Mohammed ya sara wa Jonathan, har yana kiransa da sadauki.

A ranar Talata, Jonathan yace wasu abokansa da abokan hamayyarsa na siyasa sunyi masa mummunan zato kafin zaben shugaban kasa na 2015 saboda dagewarsa da burinsa na ciyar da kasarnan gaba.

Duk da hakan, yace bai rike kowa a zuciyarsa ba, duk da kushe da zagon kasar da aka yi ta masa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel