'Yan sanda sun sake damke mutumin da yayi bidiyon da ya tada zanga-zangar EndSARS
- 'Yan sanda sun kara kama Nicholas Makolomi a jihar Delta, dan bangaren kudu-kudu a Najeriya
- Ana zargin Makolami da daukar bidiyon 'yan sanda suna kashe wani mai zanga-zangar EndSARS
- Sun tafi dashi babban birnin tarayya Abuja, duk da babbar kotun tarayya ta umarci a sake shi tun farko
Jaridar Vanguard ta ruwaito yadda ake zargin wani mutum da daukar bidiyon wasu 'yan sanda suna kashe wani mai zanga-zangar EndSARS a cikin kasarnan, Nicholas Makolomi, wanda bidiyon ya karade ko ina a kafafen sada zumuntar zamani.
An damkesa a ranar Litinin, 14 ga watan Disamba, aka zarce da shi Abuja. Kamar yadda rahoton yazo, jami'an FIB ne suka tafi dashi babban birnin tarayya.
Lauyansa, Ekenemolise Osifo, ya ce kara damkarsa a Asaba duk da babbar kotun tarayya bata amince da kama shi da rike shi tun farko ba, hakan yin karantsaye ne da doka da kuma saba wa umarnin kotu da 'yan sandan suka yi. Tuni 'yan Najeriya suka fara cece-kuce a kan kama mutumin.
KU KARANTA: FG ta nada sabon kwamitin tantance farashin man fetur, za a samu sabon farashi
Wani Abdul-Rahman Abubakar ya ce: "Su bar wannan mutumin su mayar da hankali wurin gano masu garkuwa da mutanen da suke amsar kudade daga mutane bayan yin ciniki ta waya."
Chizoba Utamazi ya ce: "Har yanzu ba a kama wani mai garkuwa da mutane ba, balle a kara kama shi a karo na biyu."
Peter Ogwola tambaya yayi: "Yanzu ya makomar daliban da aka sace? Amma hankalinsu yana kan masu zanga-zangar EndSARS."
KU KARANTA: Satar 'yan makaranta: Wasu daliban na cigaba da bullowa daga daji, Mai ba Gwamna shawara
A wani labari na daban, iyayen daliban GSSS Kankara da ke jihar Katsina, wadanda aka sace sun taru sun yi makil a harabar makarantar suna jiran komawar yaransu kamar yadda gwamnati tayi musu alkawari.
Sun taru ne bayan 'yan kwanaki kadan da faruwar lamarin, wanda satar yaran ya girgiza kowa a kasar nan. Iyayen suna ta zaman jiran ganin dawowar yaransu.
Yayin da 2 daga cikin iyayen suke tattaunawa da gidan talabijin din Channels, sun ce sun kasa barci. Sun kara da bayyana yadda za su cigaba da zama a makarantar har ranar da yaransu zasu koma garesu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng