Majalisar wakilai: Honarabul Tajuddeen ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, ya bayyana dalili

Majalisar wakilai: Honarabul Tajuddeen ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, ya bayyana dalili

- 'Yan siyasa na cigaba da sauya sheka zuwa manyan jam'iyyun kasar nan a shirinsu na tunkarar zaben 2023

- Wasu mambobin jam'iyyun adawa sai sauya sheka suke yi zuwa jam'iyyar APC mai mulki don samun alfarma a zaben gaba

- Kazalika, wasu mambobin jam'iyyar APC mai mulki sun fice zuwa jam'iyyun adawa bisa wasu dalilai na kashin kansu

Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Idanre/Ifedore a majalisar wakilai, Tajudeen Adeyemu Adegunsonye, ya sauya sheka daga jam'iyyarsa ta SDP zuwa jami'yya mai mulki, APC.

Adegunsonye, ya sanar da canza sheka tasa ranar Laraba 16 ga watan Disamba, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

Ya alaƙanta dalilin ficewar tasa da rikicin shugabanci wanda ya ki ci ya ki cinyewa a jam'iyya SDP.

KARANTA: Siyasar Kano: An yi hannun riga tsakanin Ganduje da Sha'aban Sharada

Shugaban majalisar wakilai ta tarayya, Femi Gbajabiamila, ne ya karanta wasikar ficewar dan majalisar a zauren Majalisar wakilai.

Majalisar wakilai: Honarabul Tajuddeen ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, ya bayyana dalili
Majalisar wakilai: Honarabul Tajuddeen ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, ya bayyana dalili @APC News
Asali: Facebook

A bangare guda, Anselm Ojezua, shugaban tsohon wani sashe na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Edo, ya koma jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

KARANTA: Rufe layukan waya: Yadda za ku duba ko an hada layinku da NIN daga wayoyinku na hannu

Rahotanni sun ruwaito cewa Ojezua ya jagoranci wasu mambobin jam'iyyar ta APC zuwa PDP inda ya ce ya fice ne saboda rashin gamsuwa da kamun ludayin shugabannin jam'iyyar na kasa.

A ranar 15 ga watan Disamba ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa Shugaban majalisar dokokin jihar Kano da shugaban masu rinjaye sun yi murabus daga mukamansu.

Abdulaziz Garba Gafasa, shugaban majalisar, ya sanar da cewa ya yi murabus a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 14 ga watan Disamba.

Tuni wasu rahotannin su ka wallafa cewa akwai kimanin mambobin majalisar dokokin jihar Kano 12 'yan APC da ke shirin komawa PDP.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng