Babban Sufetan ƴan sanda na ƙasa ya bada umarnin baza jami'an rundunar SWAT

Babban Sufetan ƴan sanda na ƙasa ya bada umarnin baza jami'an rundunar SWAT

- Sabbin Jami'an sabuwar rundunar SWAT za su shigo gari a karo na farko bayan kammala basu horo

- An kafa rundunar SWAT bayan rushe rundunar SARS mai yaki da fashi da makami

- Rundunar 'yan sanda ta soke SARS bayan wata zanga-zanga mai zafi da ta karada sassan Nigeria

Mohammed Adamu, babban Sufetan ƴan sandan Najeriya(IGP), ya bada umarnin baza jami'an tawagar rundunar SWAT a faɗin ƙasa don gudanar da sintiri akai akai.

A cewar rahoton da HumAngle ta wallafa, ta nuna wata wasiƙa da babban sufeta ya saki wadda ta ke umarnin a baza jami'an don fara ayyukansu;

"Babban sufetan ƴansanda ya na umartar dukkanin waɗanda aka zaɓo kuma suka sami horo a matsayin jami'an tawagar SWAT a baza su a wuraren da ya dace don fara gudanar da ayyukansu nan take."

Wasiƙar an turata ne zuwa dukkanin mataimakan sufetan ƴansanda 17 da suke faɗin ƙasar.

KARANTA: Da ma can bai cancanta ba; a karshe, Ganduje ya bayyana dalilin nada Sanusi da tsige shi

A ranar 11 ga watan Oktoba, babban sufetan ƴansanda ya sanar da wargaza rundunar ta musamman mai yaƙi da fashi da makami(SARS) bayan ɓarkewar zanga-zanga a faɗin ƙasa da kiran a kawo ƙarshen zalunci da tozarci gami da cin zarafin da SARS ke aikatawa a faɗin kasa.

Babban Sufetan ƴan sanda na ƙasa ya bada umarnin baza jami'an rundunar SWAT
Babban Sufetan ƴan sanda na ƙasa ya bada umarnin baza jami'an rundunar SWAT @Premiumtimes
Source: Twitter

"A wani yunƙurin ɗabbaƙa dimokaraɗiyya don inganta alaƙar ƴan sanda da ƴan ƙasa, babban sufeta ya bada umarnin wargaza rundunar ƴan sanda ta SARS a faɗin jihohi 36 da babban birnin tarayyar Abuja inda ake ta dambarwar," kamar yadda jawabin Frank Mba, kakakin rundunar ƴansanda ya wallafa.

"Babban sufetan, bayan watsa rundunar da ya yi, ya bada umarnin a tarwatsa jami'an SARS da aka wargaza zuwa wasu rundunonin nan take."

KARANTA: An dakatar da shugaban kwalejin kimiyya da fasaha bayan gano katafaren gado girke a ofishinsa

"Bayan an yi hakan ne rundunar ƴan sanda a ranar 12 ga watan Oktoba ta sake ƙirƙirar sabuwar runduna mai suna SWAT wadda zata maye gurbin rundunar SARS da aka wargaza."

Frank Mba, a cikin wani jawabi, ya sanar da cewa "sabuwar rundunar da aka ƙirƙira za'a basu horo cikin dabaru kana ayi musu gwajin ƙwaƙwalwa da zai tabbatar da lafiyar hankalinsu da jikinsu sannan kuma ya bada damar ɗaukar su aikin."

"Dukkan mutanen da aka zaɓa za'a yi musu gwajin lafiya da hankali don tabbatar da lafiyarsu da kuma bada damar ɗaukarsu aikin. Zasu fara ɗaukar horo a dukkanin wuraren horon da ke faɗin ƙasa daga sati mai zuwa acewar Mba."

A farkon watan Oktoba ne ƴan Najeriya suka fara ƙaddamar da zanga-zanga mai taken #EndSARS don kawo ƙarshen tozarci, zalunci da cin zarafin al'umma da jami'an SARS ke yi.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa CNG sun ce zasu yi tattaki zuwa garin Daura, mahaifar shugaban kasa, Muhamadu Buhari, domin fara zaman dirshan akan sace dalibai akalla 333 a sakandiren kimiyya da ke Kankara, jihar Katsina.

Fiye da dalibai 300 ne ake zargin cewa su na hannun 'yan bindigar da suka shiga cikin dakunansu na kwana suka yi awon gaba da su.

'Yan bindigar sun dira makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara, jihar Katsina, da talatainin daren Juma'a zuwa duku-dukun safiyar Asabar, tare da yin awon gaba da dalibai kusan 600.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel