Tsoffin sanatoci da 'yan majalisu suna zawarcin Tinubu don shugabanci kasa a 2023

Tsoffin sanatoci da 'yan majalisu suna zawarcin Tinubu don shugabanci kasa a 2023

- Wata kungiya ta tsofaffin sanatoci 'yan majalisar kudu suka hada ta fara yi wa Tinubu kamfen

- A ranar Litinin, jiga-jigan kungiyar suka kaiwa Oba Saliu Adetunji da Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi III, ziyara

- Sun ce dama akwai yarjejeniyar da shugabannin APC suka yi a 2014 na baiwa 'yan kudu damar takara a 2023

Wata kungiya ta fara kamfen a ranar Litinin ta hanyar kai ziyara ga sarakunan gargajiya kamar Olubadan na Ibadan, Oba Saliu Adetunji da Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi III, inda suka sanar da sarakunan manufarsu.

Kungiyar ta tattaro mambobinta don su cika burin kudu maso yamma, na samar da shugaban kasa a 2023, The Nation ta wallafa.

Cikin kungiyar akwai Sanata Adesoji Akanbi a matsayin mataimakin kungiyar da Bosun Oladele a matsayin sakatare.

Tsoffin sanatoci da 'yan majalisu suna zawarcin Tinubu don shugabanci kasa a 2023
Tsoffin sanatoci da 'yan majalisu suna zawarcin Tinubu don shugabanci kasa a 2023. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: FG ta nada sabon kwamitin tantance farashin man fetur, za a samu sabon farashi

Sauran mambobin sun hada da Otunba Abayomi Ogunnusi, Kafilat Ogbara, Oyetunde Ojo, Deji Jakande da Ifedayo Abegunde, wato Abena, Sanata Musiliu Obanikoro da Adeseye Ogunlewe.

Bola Tinubu, tsohon gwamnan Legas ne, kuma jagaba a jam'iyyar APC. Shi ya tsaya tsayin-daka wurin tsayar da Muhammadu Buhari a matsayin dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC a 2014.

Adeyeye ya sanar da shugabannin cewa kungiyar SWAGA an kirkireta ne don tabbatar da samun shuganan kasa a kudu maso yamma, idan tayi nasara ta gaji shugaba Buhari a 2023.

KU KARANTA: Ana tsaka da matsalar tattalin arziki, mazauna Guaca sun samu ziinarai da zurfa a kauye kauyensu

Ya ce Asiwaju Tinubu yana da duk wasu halaye da gogewa da yakamata a ce shugaban kasa ya samu. Sannan ya bayyana irin yarjejeniyar da shugabannin APC suka yi lokacin zaben 2015 na tsarin karba-karba da kudu, idan Buhari ya karasa shekarunsa 8 a kan mulki.

Don haka sun ce sun je wurin shugabannin ne don su nemi goyon baya, sannan suna sane da cewa hakkinsu ne samar da wani shugaban kasar. Kuma suna fatan Ubangiji ya bai wa Buhari tsawon rai har ya karasa mulkinsa, don ya baiwa kudu damar mulkar Najeriya.

A wani labari na daban, majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da fara daukar ma'aikata 774,000 na ayyuka na musamman da za ta fara a watan Janairun 2021.

Majalisar kuma ta bukaci ma'aikatar kudi da ta dakatar da sakin kudaden da ya kamata a yi amfani dasu don shirin har sai an kammala bincike a kan wasu matsaloli da suka taso na ingancin shirin.

Hon. Olajide Olatubonsun ya daga batun a majalisar saboda ya shafi al'umma, sannan majalisar ta kunshi sauke shugaban NDE, Mohammed Kadan Argungu, inda tace a yi gaggawar mayar dashi mukaminsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel