FG ta nada sabon kwamitin tantance farashin man fetur, za a samu sabon farashi

FG ta nada sabon kwamitin tantance farashin man fetur, za a samu sabon farashi

- Gwamnatin tarayya ta samar da kwamitin da zai dinga kulawa da farashin man fetur

- Ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige, ya ce gwamnati bata riga ta tsayar da farashin ba

- Amma ya ce ana sa ran kwamitin za ta bayyana rahoton da za a duba a ranar 25 ga watan Janairun 2021

Gwamnatin tarayya ta samar da wani kwamiti wanda zai dinga kulawa da tsayar da farashin man fetur.

Hakan ya biyo bayan sanar da sabon farashin mai na PMS da gwamnati tayi a makon da ya gabata, inda ta sanar da farashin a ranar Litinin.

Sanarwar ta biyo bayan taron kwamitin da gwamnatin tarayya, wanda NLC ta shirya da kungiyar kasuwanci don fitar da tsayayyen farashin man fetur, jaridar Punch ta wallafa.

A ranar 8 ga watan Disamba an rage farashin man fetur da N5, maimakon N168 zuwa N162.44 kowacce lita tun daga ranar 14 ga Disamba.

KU KARANTA: JNI ta fallasa wadanda basu son a kawo karshen rashin tsaro a Najeriya

FG ta nada sabon kwamitin tantance farashin man fetur, za a samu sabon farashi
FG ta nada sabon kwamitin tantance farashin man fetur, za a samu sabon farashi. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

Amma a ranar Litinin da ta gabata kwamitin ta kaddamar, sai dai ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige, ya ce har yanzu gwamnati bata riga ta tsayar da kudin fetur ba. A cewarsa, "An samu ragi ne a kudaden kaiwa da komawa da man, da kuma na lodi da ajiyar man."

Ngige ya kara da cewa, "Ana sa ran kwamitin za ta gabatar da rahoto a ranar Litinin, 24 ga watan Janairun 2021, sai dai da farko kwamitin za ta fara duba abubuwa kamar farashin kudin wutar lantarki da sauransu.

"Ana sa ran kwamitin za ta yi aiki tukuru wurin samar da tsayayyen farashin man fetur."

Mambobin kwamitin sun hada da shugaban kwamitin, Onochie Anyaoku, da sakataren kungiyar, Lawal Musa daga NNPC.

KU KARANTA: Da duminsa: Gwamnan APC ya garzaya Amurka duba lafiya, zai kwashi makonni 2

A wani labari na daban, daya daga cikin daliban GSSS Kankara na jihar Katsina, wanda ya samu ya tsere daga hannun 'yan ta'adda ya ce 'yan ta'addan sun kashe 2 daga cikin daliban.

Daya daga cikin iyayen yaran da ke hannun 'yan ta'addan, Faiza Hamza Kankara, ta sanar da hakan, inda tace wanda ya tsere daga hannun 'yan ta'addan ne ya sanar dasu hakan.

Matar wacce take cikin matsananciyar damuwa ta ce dalibin ya sanar dasu yadda 'yan bindigan suke ciyar dasu ganye kuma suke dukansu kamar shanu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng