Korona ta harbi sabbin mutane 758 a Nigeria, fiye da mutum 100 a Kaduna

Korona ta harbi sabbin mutane 758 a Nigeria, fiye da mutum 100 a Kaduna

- Alamu na nuni da cewa da gaske annobar korona ta sake yunkurowa a karo na biyu

- Alkaluman masu kamuwa da kwayar cutar sai kara hawan gwauron zabi suke yi a 'yan kwanakin baya bayan nan

- Tuni Jihohi suka fara bayar da umarnin rufe makarantu, musamman na Firamare da Sakandire

Alkaluman baya bayan nan akan mutanen da annobar cutar korona ke kamawa a Nigeria suna saka damuwa a zukatan jama'a tare da fargabar cewa za'a koma gidan jiya.

Mutane 758 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Talata, 15 ga watan Disamba, kamar yadda ya ke a sakon sanar da alkaluman sabbin mutane da cutar ke kamawa wanda NCDC ta saba fitarwa kullum.

Sanarwar ta nuna cewa alkaluman wadanda suka kamu da kwayar cutar a babban birnin tarayya, Abuja, sun ninka adadin wadanda kwayar cutar ta harba a jihar Legas.

KARANTA: Katsina: Boko Haram ta dauki alhakin sace daliban Kankara, ta fadi dalili

Daga jihar Kaduna, mutane 103 ne sakamakon gwajinsu ya nuna cewa suna dauke da kwayar cutar.

Korona ta harbi sabbin mutane 758 a Nigeria, fiye da mutum 100 a Kaduna
Korona ta harbi sabbin mutane 758 a Nigeria, fiye da mutum 100 a Kaduna @NCDC
Asali: Facebook

Ga jerin jihohin da adadin mutanen da suka kamu da kwayar cutar a jihohin da sunayensu suka bayyana a sanarwar NCDC ta daren ranar Talata.

Jimillar sabbin mutane 758 sun kamu da kwayar cutar #COVID19 a Nigeria;

FCT-305

Lagos-152

Kaduna-103

Bauchi-44

Gombe-35

Plateau-31

Rivers-17

Sokoto-15

Kwara-13

Kano-9

Ebonyi-8

Ogun-5

Osun-5

Oyo-4

Edo-4

Anambra-4

Bayelsa-2

Ekiti-1

Taraba-1

Ya zuwa karfe 11:13 na daren ranar Talata, jimillar mutum 74,132 aka tabbatar da cewa sun kamu da kwayar cutar korona a sassan Nigeria.

KARANTA: Da ma can bai cancanta ba; a karshe, Ganduje ya bayyana dalilin nada Sanusi II da tsige shi

Daga cikin Jimillar mutanen, an sallami mutum 66,494 bayan an tabbatar cewa sun warke, sun samu lafiya.

Kalika, kwayar cutar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 1200.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da rufe makarantun firamare da sakandare mallakar gwamnati da masu zaman kansu da ke cikin jihar.

Ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun daga ranar Talata, sakamakon cigaba da yaduwar cutar COVID-19 a kasar nan.

Mukaddashin sakataren ma'aikatar ilimi, kimiyya da fasaha, na jihar, Rabiu Adamu, shine ya sanar da hakan ta wata takarda da ya bai wa manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel