Kankara: Iyayen dalibai sun jeru a farfajiyar makaranta suna jiran dawowar 'ya'yansu
- Iyayen daliban GSSS Kankara da aka sace sun taru a harabar makarantar suna jiran yaransu su koma garesu
- Wasu daga iyayen sun bayyana cewa basa iya yin barci, saboda tsananin tashin hankalin da suke ciki
- Sun ce suna zaman jiran gwamnati ta cika musu alkawarin da ta daukar musu na ceto yaran daga hannun 'yan ta'addan
Iyayen daliban GSSS Kankara da ke jihar Katsina, wadanda aka sace sun taru sun yi makil a harabar makarantar suna jiran komawar yaransu kamar yadda gwamnati tayi musu alkawari.
Sun taru ne bayan 'yan kwanaki kadan da faruwar lamarin, wanda satar yaran ya girgiza kowa a kasar nan.
Iyayen suna ta zaman jiran ganin dawowar yaransu. Yayin da 2 daga cikin iyayen suke tattaunawa da gidan talabijin din Channels, sun ce sun kasa barci. Sun kara da bayyana yadda za su cigaba da zama a makarantar har ranar da yaransu zasu koma garesu.
KU KARANTA: Da kudin siyan iPhone 12 Pro Max, matashi ya bude gagarumin wurin siyar da tsire
Bayan wakilinmu ya isa makarantar, ya fahimci cewa makarantar Kankara tana tsakiyan dajin da zai kai mutum har Zango da Damsadau wurin da suke da iyaka da jihar Zamfara.
Sannan an tattaro bayanai a kan yadda ta gefen katangar makarantar akwai wani babban titi wanda zai kai mutum har kasuwar Kankara ta ranar Talata don saye da siyarwa.
Yau da safe, 17 daga cikin dalibai 333 sun koma gidajensu, wadanda suka samu nasarar tserewa daga hannun wadanda suka sacesu, hakan yana nufin akwai sauran 316 a hannunsu.
KU KARANTA: Budurwa ta fusata bayan saurayinta da ya ci cacar N20m ya bata N20,000
A wani labari na daban, mai baiwa gwamnan jihar Katsina shawara na musamman, Alhaji Abdulaziz Maituraka, ya ce cikin daliban GSSS Kankara na jihar Katsina da suka bata, wasu sun bullo daga daji.
BBC Hausa ta ruwaito hakan a ranar Talata, inda ta bayyana cewa 'yan bindiga sun sace dalibai fiye da 500, Vanguard ta wallafa.
Mai bayar da shawarar na musamman ya ce basu da masaniya a kan batun shugaban 'yan Boko Haram.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng