Budurwa ta fusata bayan saurayinta da ya ci cacar N20m ya bata N20,000

Budurwa ta fusata bayan saurayinta da ya ci cacar N20m ya bata N20,000

- Wata budurwa 'yar Najeriya ta wallafa irin takaicin da saurayinta ya sanya mata a zuciya

- Ta ce ya sami N20,000,000 ta hanyar caca, amma ya rasa kudin da zai bata sai N20,000

- Budurwar ta ce a zaton ta zai warware a kalla N1,000,000 a cikin kudin ya bata

Idan mutane 2 suna soyayya, batun kudi yana zama babbar matsala musamman idan daya daga cikin masoyan yana sanya mako a harkar.

Wata budurwa mai suna Reddishwine3, ta wallafa irin takaicin da saurayinta ya sanya mata a zuciya a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.

A cewarta, saurayinta ya samu zunzurutun kudade har N20,000,000, a harkar caca. Maimakon ya cire a kalla N1,000,000 a cikin kudin ya bata, sai ya dauki N20,000 ya bata.

Budurwa ta fusata bayan saurayinta da ya ci cacar N20m ya bata N20,000
Budurwa ta fusata bayan saurayinta da ya ci cacar N20m ya bata N20,000. Hoto daga @Reddishwine3
Asali: Twitter

KU KARANTA: UN ta magantu a kan satan 'yan makarantan Kankara, ta bada muhimmin umarni

Wannan abu da saurayin yayi ya fusata budurwar kwarai.

Mutane da dama sun yi ta cece-kuce a karkashin wallafar, inda wata Lola Okunrin tace, "Kila saurayin bai damu da budurwar bane, har da ya kasa cire fiye da N20,000 a cikin kudin ya bata."

Wata Mimi, cewa tayi, "Gaskiya da saurayina ne da fiye da rabin kudin zai bani."

Amma ta shawarci budurwar a kan tayi hakuri tun da ma ta samu ya bata wani abu cikin kudin. Ta ce wasu samarin ba za su baka ko sisi ba. Ta kwantar da hankali har itama ta samu nata N20,000,000 din.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Farfesa ya bukaci gwamnati da ta diba mafarauta aikin tsaro

A wani labari na daban, 'yan bindiga sun yi garkuwa da a kalla mutane 19 a garin Ogu da Tegina da ke karamar hukumar Rafi a jihar Neja.

Shugaban ma'aikatan shugaban karamar hukumar Rafi, Mohammed Mohammed, ya tabbatar wa da gidan talabijin din Channels faruwar lamarin a ranar Litinin.

Har kiran wasu daga cikin mazauna unguwannin don samun karin bayani a kan al'amarin, Channels TV ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng