Satar 'yan makaranta: Wasu daliban na cigaba da bullowa daga daji, Mai ba Gwamna shawara

Satar 'yan makaranta: Wasu daliban na cigaba da bullowa daga daji, Mai ba Gwamna shawara

- Mai baiwa gwamnan jihar Katsina shawara na musamman, Alhaji Abdulaziz Maituraka, yace wasu daga cikin daliban GSSS sun bullo ta daji

- A cewarsa, basu da wata masaniya game da maganar Shekau, wanda yace shi da yaransa ne suke da alhakin sace yaran

- Ya ce kamar yadda mutane suka ga bayanin, haka suma suka gani, suna neman addu'ar jama'a kuma a daina yada labaran bogi

Mai baiwa gwamnan jihar Katsina shawara na musamman, Alhaji Abdulaziz Maituraka, ya ce cikin daliban GSSS Kankara na jihar Katsina da suka bata, wasu sun bullo daga daji.

BBC Hausa ta ruwaito hakan a ranar Talata, inda ta bayyana cewa 'yan bindiga sun sace dalibai fiye da 500, Vanguard ta wallafa.

Mai bayar da shawarar na musamman ya ce basu da masaniya a kan batun shugaban 'yan Boko Haram.

Satar 'yan makaranta: Wasu daliban na cigaba da bullowa daga daji, Mai ba Gwamna shawara
Satar 'yan makaranta: Wasu daliban na cigaba da bullowa daga daji, Mai ba Gwamna shawara. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon Buhari ya ziyarci shanunsa a Daura ya janyo cece-kuce

Dama Abubakar Shekau ya ce shi da sauran 'yan Boko Haram ne suka sace yaran GSSS Kankara. Ya ce kamar yadda mutane suka gani, haka suka gani a kafar sada zumuntar zamani.

"Mun ga yadda 'yan Boko Haram suka ce su ne suka sace yaran a kafafen sada zumuntar zamani. Amma ko ma menene, muna addu'ar Allah ya dawo mana da yaran lafiya."

A kan labarin cewa gwamnati ta fara tattaunawa da 'yan bindiga ta yadda za ta ceto yaran, yace yakamata mutane su kiyaye yada labarai marasa inganci da kuma abinda jami'an tsaro basu ce ba.

KU KARANTA: Budurwa ta fusata bayan saurayinta da ya ci cacar N20m ya bata N20,000

"Jami'an tsaro suna daji, idan akwai abinda muke bukata a wurin jama'a, addu'a ce," a cewarsa.

Duk da dai iyayen yaran suna cigaba da tuntubar makarantar don jin labarin yaransu da suka bata.

A wani labari na daban, tsohuwar ministar ilimi, Oby Ezekwesili, ta ce Najeriya bata da shugabanni a yanzu tunda har aka iya satar dalibai fiye da 300 a GSSS Kankara, da ke jihar Katsina, The Punch ta wallafa.

Tsohuwar ministar, ta tsaya tsayin-daka wurin yin zanga-zanga don a ceto fiye da mata 250 'yan makaranta daga Chibok, jihar Borno a shekarun da suka gabata.

Ta ce wannan satar yaran da aka yi alama ce ta rashin shugabanni nagari masu tafiyar da lamuran kasar nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel