Da kudin siyan iPhone 12 Pro Max, matashi ya bude gagarumin wurin siyar da tsire

Da kudin siyan iPhone 12 Pro Max, matashi ya bude gagarumin wurin siyar da tsire

- Wani saurayi mai suna Asim Balarabe Yazid ya yi wata wallafa a kafar sada zumunta, dalilin haka mutane suka yi ta yaba masa

- Asim ya ce ya fara sana'ar gasa nama a Kano, inda ya dauki masu taya shi aiki mutane 3

- Ya yi amfani da kudin da yakamata ya siya waya IPhone 12 Pro Max wurin fara sana'ar

Wani saurayi mai suna Asim Balarabe Yazid ya baiwa matasa kwarin guiwa, inda yace maimakon mutum ya warware kudade masu yawa ya siya waya, gara yayi amfani da kudaden don ya fara sana'a dasu.

A cewarsa, har daukar ma'aikata 3 yayi suna aiki a karkashinsa. Ya ce sana'arsa tana ta bunkasa, yanzu haka yana da kudaden da zaiyi amfani da su ya biya ma'aikatansa na watanni 3. Kuma yace yana adana ribar da yake samu maimakon kashewa gaba daya.

'Yan Najeriya da dama sun yaba wa irin tunaninsa, inda suka ce ya yi kokari kwarai da yayi wannan tunanin.

Da kudin siyan iPhone 12 Pro Max, matashi ya bude gagarumin wurin siyar da tsire
Da kudin siyan iPhone 12 Pro Max, matashi ya bude gagarumin wurin siyar da tsire. Hoto daga @asimyaz
Source: Twitter

KU KARANTA: Rashin tsaro: Farfesa ya bukaci gwamnati da ta diba mafarauta aikin tsaro

Wani Abba_GT cewa yayi, "Wannan alama ce ta wanda ya san naira ta lalace, kuma hakan ya faru ne sakamakon yadda muke amfani da kudadenmu ne, ba gwamnati kadai ba.

"Idan da a kalla matasa 40% za su yi irin wannan tunanin na shi, da komai ya canja."

Da sauran mutane da suka yi ta yaba wa dabararsa da kuma yi masa fatan alheri.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace mutum 19, sun halaka fasto a Niger

A wani labari na daban, idan mutane 2 suna soyayya, batun kudi yana zama babbar matsala musamman idan daya daga cikin masoyan yana sanya mako a harkar.

Wata budurwa mai suna Reddishwine3, ta wallafa irin takaicin da saurayinta ya sanya mata a zuciya a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.

A cewarta, saurayinta ya samu zunzurutun kudade har N20,000,000, a harkar caca. Maimakon ya cire a kalla N1,000,000 a cikin kudin ya bata, sai ya dauki N20,000 ya bata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel