Satar 'yan makarantan Kankara: Babu gwamnati a kasar nan, Ezekwesili

Satar 'yan makarantan Kankara: Babu gwamnati a kasar nan, Ezekwesili

- Tsohuwar ministan ilimi, Oby Ezekwesili ta ce Najeriya bata da shugabanni

- Ta fadi hakan ne bayan samun labarin satar daliban GSSS Kankara da ke jihar Katsina

- Ta bayyana wannan ra'ayin nata ne a wata hira da BBC tayi da ita ranar Talata

Tsohuwar ministar ilimi, Oby Ezekwesili, ta ce Najeriya bata da shugabanni a yanzu tunda har aka iya satar dalibai fiye da 300 a GSSS Kankara, da ke jihar Katsina, The Punch ta wallafa.

Tsohuwar ministar, ta tsaya tsayin-daka wurin yin zanga-zanga don a ceto fiye da mata 250 'yan makaranta daga Chibok, jihar Borno a shekarun da suka gabata.

Ta ce wannan satar yaran da aka yi alama ce ta rashin shugabanni nagari masu tafiyar da lamuran kasar nan.

Bayan an tambayeta idan tana ganin gwamnati za ta iya kawo karshen rashin tsaronnan, cewa tayi bata fahimci gwamnatin da ake magana ba. Don kasar nan ba ta da wata gwamnati a halin yanzu.

KU KARANTA: 2023: Magoya bayan Tinubu sun kai ziyarar neman goyon baya fadar babban basarake

Satar 'yan makarantan Kankara: Babu gwamnati a kasar nan, Ezekwesili
Satar 'yan makarantan Kankara: Babu gwamnati a kasar nan, Ezekwesili. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: IPMAN ta jihar Kano ta bada sabon farashin litar man fetur

Ezekwesili ta ce al'amarin ya kazanta, ta yadda aka sace dalibai masu yawan gaske. Ta tunatar da lokacin da aka sace Leah Sharibu, daga Dapchi na tsawon shekaru.

Ta ce idan 'yan Najeriya suka cigaba da amincewa da wannan zaluncin, tabbas babu ranar da zai zo karshe.

A wani labari na daban, wani dan Najeriya mai suna Mustapha Yusuf ya yi tattaki tun daga jihar Sokoto har jihar Bauchi, don nunawa gwamna Bala Mohammed kauna sakamakon nasarorin da ya samu tun bayan hawansa mulki.

Gwamnan ya baiwa Yusuf kyautar mota kirar Peugeot 406 a matsayin kyauta don nuna farin cikinsa.

Mutumin ya yi tattakin ne don ya yabawa gwamnan a kan cigaban da ya samar a jiharsa, inda yake kara masa kwarin guiwa a kan ya cigaba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel