2023: Magoya bayan Tinubu sun kai ziyarar neman goyon baya fadar babban basarake

2023: Magoya bayan Tinubu sun kai ziyarar neman goyon baya fadar babban basarake

- Amimtattun 'yan siyasar Bola Tinubu sun fara yi masa kamfen din shugabancin kasa na 2023

- Sun nufi fadar Alaafin na jihar Oyo, don neman hadin kan Alaafin Lamidi Adeyemi, kuma ya mara musu baya

- Ya tabbatar musu da yadda yake tare dasu dari bisa dari, duk da sun ce Tinubu bai san sun je ba

Amintattun 'yan siyasar Bola Tinubu, shugaban jam'iyyar APC, sun kai wa Lamidi Adeyemi, Alaafin din Oyo ziyara a ranar Litinin.

Dayo Adeyeye, tsohon ministan ayyuka shine ya jagoranci ziyarar, kungiyar, inda suka ce sunje fadar ne don samun hadin kai don marawa Tinubu baya wurin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Soji Akanni, tsohon sanatan jihar Oyo; Rotimi Makinde, tsohon dan majalisar wakilai; Oyetunde Oko, mijin diyar Bola Tinubu, duk suna cikin wadanda suka kai ziyara fadar Saliu Adetunji, Olubadan din Ibadan.

KU KARANTA: BringBackOurBoys: Kungiyar arewa ta fara tattaki don samun Buhari a Daura

2023: Magoya bayan Tinubu sun kai ziyarar neman goyon baya fadar babban basarake
2023: Magoya bayan Tinubu sun kai ziyarar neman goyon baya fadar babban basarake. Hoto daga @Thecableng
Source: Twitter

Yayin da suke jawabi ga sarkin a fadar, Adeyeye ya ce Tinubu yana da damar gadar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya ce tun da dokar APC ta amince wa kudu tsayawa takara, yakamata Yarabawa su mara wa Tinubu baya.

Adeyeyi ya ce Tinubu bai san suna fafutukar yakin nema masa hadin kai ba.

A cewarsa, "Muna da burin siyasa, ya kamata a ce Yarabawa sun samu damar mulkar Najeriya,"

"Mun yi yarjejeniya cewa bayan shugaba Muhammadu Buhari yayi shekaru 5, Yarabawa za su amshi mulki.

Alaafin din ya ce ya yarda da al'amarin da kungiyar ta zo masa dashi.

A cewarsa, "A kasar Yarabawa, mun yarda da kwanciyar hankali. Mun yarda da adalci. Wani zai iya yin tunanin cewa munyi gaggawar fara kamfen din shugabancin 2023, amma bai yi wuri ba."

"Satin da ya gabata, 'yan Boko Haram sun yi wa mutane yankan rago, ba za mu amince da hakan ba, muna bukatar cigaba," a cewarsa.

KU KARANTA: Satar 'yan makaranta: Dalibai 668 ne har yanzu babu, Hukumar makaranta

A wani labari na daban, UN ta yi kira a kan gaggawar sakin daliban GSSS Kankara da ke jihar Katsina a ranar 14 ga watan Disamban 2020, Channels TV ta wallafa.

UN ta nuna takaicin ta ne dangane da satar daliban GSSS Kankara da ke jihar Katsina, bayan 'yan bindiga sun kai farmaki makarantar.

Majalisar dinkin duniya ta yi wannan kiran a wata takardar da kakakin babban sakataren, Stephanie Dujarric, ya saki a ranar Litinin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel