Ba za mu yarda da irin wannan kashe-kashen jama'a ba; Tinubu ya fusata

Ba za mu yarda da irin wannan kashe-kashen jama'a ba; Tinubu ya fusata

- Jagoran jam'iyyar APC kuma tsohon gwamna a jihar Legas, Bola Tinubu, ya ziyarci jihar Borno

- Tinubu ya ziyarci Borno ne domin jajajantawa gwamnan jihar, Farfesa Babagana Zulum, kisan manoma fiye da 43

- A cewar Tinubu, Nigeria ba zata lamunci kashe-kashen jama'a yayin da suka fita neman abincinsu ba

Tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagora a jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya yi kalamai cikin fushi dangane da kashe-kashen da 'yan ta'adda ke yi a sassan kasa.

Tinubu ya bayyana cewa Nigeria ba zata yarda hakan ta cigaba da faruwa ba, kamar yadda Newswirengr.com ta rawaito.

Babban dan siyasar ya bayyana hakan ne a Maiduguri yayin da ya ziyarci gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, domin yi masa jajen kisan manoma fiye da 43 da 'yan Boko suka yi.

A kalla manoma fiye da 48 aka bayyana, a hukumance, cewa an kashe a gonakinsu na gona Zabarmari, jihar Borno.

KARANTA: An kulla yarjejeniya tsakanin Buhari da Tinubu akan kujerar shugaban kasa

Da yake magana da manema labarai a gidan gwamnatin jihar Borno, Tinubu ya ce ba za'a taba samun cigaba a wurin da rayukan jama'a ke fuskantar barazana ba.

Ba zamu yarda da irin wannan kashe-kashen jama'a ba; Tinubu ya fusata
Ba zamu yarda da irin wannan kashe-kashen jama'a ba; Tinubu ya fusata @Profzulum
Asali: Twitter

"Ba za'a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali ba a wurin da ake yanka mutane yayin da suka fita neman abincinsu ba," a cewar Tinubu.

Tinubu ya bayyana cewa ya ziyarci jihar Borno ne domin jajantawa gwamna Zulum akan abinda ya faru.

KARANTA; Kakakin majalisar dokokin jihar Kano, shugaban masu rinjaye sun yi murabus

"Muna bukatar samun zaman lafiya a kasar nan, amma hakan ba zai samu ba idan ana yanka jama'a a wuraren neman abincinsu.

"Ya kamata mu jawo matasanmu a jiki, ba zamu yarda irin wannan kisan dumbin jama'a ya cigaba da faruwa ba," a cewar Tinubu.

Babban kusa a jam'iyya mai mulki, APC, ya bayyana yadda aka kulla wata yarjejeniya da aka cimma tsakanin shugabannin jam'iyyar tun shekarar 2014, kamar yadda Punch ta rawaito.

Tunde Balogun, wanda shine shugaban rikon jam'iyyar a jihar Legas, ya bayyana cewa akwai yarjejeniyar baiwa Yarabawa mulki a shekarar 2023.

Ya ƙara da cewa, Buhari da Tinubu na cikin waɗanda suka amince da wannan yarjejeniya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel