Wata Jami'ar kasar Amurka ta dauki Ganduje aiki a matsayin Farfesa

Wata Jami'ar kasar Amurka ta dauki Ganduje aiki a matsayin Farfesa

- Jami'ar 'East Carolina' da ke kasar Amurka ta aikowa gwamna Ganduje takardar daukansa aiki a matsayin Farfesa

- A cewar Jami'ar, iliminn Ganduje, kwarewa a mulki, da shaidar kirki da aka yi masa sune silar daukansa aikin

- Idan har ya amince da bukatar Jami'ar, Ganduje zai shiga sahun manyan malamanta da ke aiki a cibiyar ECU-ICITD

ECU-ICITD, wata cibiyar bunkasa fasahar sarrafa labarai ta kasa da kasa a Jami'ar East Carolina da ke kasar Amurka, ta dauki gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, aiki a matsayin Lakcara.

Jami'ar ta dauki Ganduje a matsayin babban masani da ke matakin Farfesa wanda zai ke koyar da darussan 'E-Governance' da 'International Affairs' a bisa tsarin malami mai ziyara.

Jami'ar ta ce ta zabi karrama Ganduje da wannan aiki ne domin samun damar karuwa da dumbin iliminsa, basirarsa, da kwarewa a harkar mulki.

KARANTA: A karshe: An gama wasan buya, an kama Abdulrasheed Maina a Nijar

Wani bangare na takardar daukar aiki da jami'ar ta aikowa Ganduje na cewa, "za mu ji dadi a ce koda sau daya ne a shekara za ka samu damar yin magana da dalibanmu a wurin taron bita da karawa juna sani.

Wata Jami'ar kasar Amurka ta dauki Ganduje aiki a matsayin Farfesa
Wata Jami'ar kasar Amurka ta dauki Ganduje aiki a matsayin Farfesa @Daily_trust
Asali: Twitter

"Idan har za mu fadi gaskiyarmu, mun zabeka ne saboda dumbin iliminka, kwarewar aiki, da tarihin iya jagoranci a Najeriya da nahiyar Afrika, hakan ya sa ka zama mutumin da jami'ar 'East Carolina' ke nema domin cimma muradanta a matsayin cibiyar bayar da ilimi a kasar Amurka da duniya baki daya.

KARANTA: Kaduna: An shafe dare guda ana musayar wuta tsakanin sojoji da 'yan bindiga a Jaji

A karshen wasikar, jami'ar ta bayyana cewa; "mu na fatan za ka karbi wanna aiki, ya mai girma. Da zarar mun samu takardar amincewarka, za mu saka sunanka cikin jerin manyan malamanmu a cibiyar ECU-ICITD."

A makon da ya gabata ne gwamna Ganduje ya saka hannu a kan dokar ilimi kyauta kuma dole ga dukkan yaran jihar Kano.

Kirkirar dokar ya na da nasaba da hauhawar alkaluman yaran da basa zuwa makaranta, sai gararamba da yawon bara a titunan jihar Kano.

Ganduje tsohon malamin jami'a ne a BUK kafin daga baya ya koma bangaren gudanarwa na gwamnati.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel