Mace mai dogaro da kanta bata rokon namiji, ku yi aikin hankali ku kyautata musu, Jaruma Juliet
- Wata jarumar fina-finan kasar Ghana ta shawarci maza a kan soyayya da mace mai sana'a
- A cewarta, ya kamata a ce duk namiji mai soyayya da irin wannan macen ya dinga yi mata kyauta haka nan
- Kamar yadda Juliet tace, irin matan nan basu jiran maza idan za su yi lamurransu na rayuwa
Wata fitacciyar jarumar fina-finan kasar Ghana, Juliet Ibrahim, ta bai wa maza shawara a kan soyayya ta shafinta na kafar sada zumuntar zamani.
A cewar jarumar, duk namijin da yake soyayya da mace mai sana'a yak amata ya dinga yin abubuwan da suka dace. Ba sai budurwar ta tambaye shi ba.
Jarumar ta bayyana dalilanta a kan shawarar da ta bayar, ta ce mata masu ayyukan yi basa tambayar samari kudi, idan bukata tazo, kawai cire kudi suke yi su biya bukatunsu.
KU KARANTA: Da yawan almajiran da ke tituna ba 'yan Najeriya bane, Gwamna Ganduje
Kyakkyawar jarumar ta wallafa hotunan ta a bakin ruwa, sanye da wata riga mai kyau. Take anan mutane suka hau yi mata tsokaci iri-iri a karkashin wannan wallafar tata.
Inda da yawansu suke nuna amincewarsu dari bisa dari a kan wannan shawarar.
KU KARANTA: Oshiomhole ya bayyana abinda zai yi idan ya samu damar sake shugabancin APC
A wani labari na daban, Rashidat, matar Sheriff Ahmed, mai shekaru 44, ta zargi mijinta da takura mata a kan yadda take shiga. Ahmed ya maka matarsa a kotu, inda yake bukatar su rabu sakamakon rashin kamun kanta da kuma mummunar shiga.
Ya kai korafin a wata kotu da ke Igando ranar Litinin, inda ya zargeta da lalata da wani dan sanda, The Cable ta wallafa.
A cewarsa, ya so ya fatattaki matarsa, amma yadda 'yan uwa da abokan arziki suka sanya baki yasa ya hakura.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng