BringBackOurBoys: Kungiyar arewa ta fara tattaki don samun Buhari a Daura
- A yau 'yan kungiyar CNG za su yi tattaki har zuwa Daura saboda satar daliban GSSS Kankara
- Kakakin kungiyar ya sanar da hakan, inda yace wajibi ne su samu shugaba Buhari don su nuna damuwarsu
- Ya ce 'yan kungiyar daga jihar Kano da Jigawa za su hadu da wasu 'yan kungiyar a Mashi, sai su nufi Daura
Kungiyar hadin kan arewa ta ce ta fara tattaki zuwa Daura, garin shugaba Muhammadu Buhari, don zanga-zanga a kan satar daliban GSSS Kankara a jihar Katsina.
Idan ba a manta ba, Shugaba Buhari ya isa garin Daura a ranar Jama'a, ana saura mako daya 'yan bindiga su je makarantar.
Kakakin CNG, Abdul-Azeez Suleiman a ranar Litinin ya tattauana da Punch, inda yace 'yan kungiyarsu za su isa gidan shugaban kasa yau din nan sannan har yanzu ba a ga ragowar daliban ba.
KU KARANTA: Kasashenmu suna da tsohon tarihin zumunci, Buhari ya taya shugaban kasan Ghana murnar zarcewa
Ya ce, "Yan kungiyarmu na wannan jihar za su yi tattaki har zuwa Daura a jihar Katsina don sanar da Buhari bukatarsu, don ya dauki mataki a kan wannan al'amarin tunda yana nan a Daura.
"Yan CNG na jihar Kano za su taso tun daga Dambatta don bin bayan 'yan kungiyar na jihar Katsina, sai su hadu da 'yan jihar Jigawa a Kazaure, sai su taru a Mashi, daga nan su yi tattaki zuwa Daura, don su samu Shugaba Buhari."
Kakakin ya ce sun matukar jin radadin yadda 'yan ta'adda suka yi wa 'yan arewa yankan rago.
KU KARANTA: Gwamnan APC zai dauka mataki a kan masu mukami a gwamnatin marasa saka takunkumi
A wani labari na daban, kamar yadda Mail Online ta ruwaito, wanda ake zargin, manajan wata makaranta, ya kashe £4,100,000 a kan mata 4, ciki har da matarsa da karuwansa.
Ya fara aiki a Haberdasher, wacce take da jibi da makarantun gwamnati masu irin sunanta a 1997, The Cable ta wallafa.
Thacker ya ce a 2006, Kayode ya fara amfani da tsarin tura kudi na BACS wurin hankada wa matarsa Grace kudade, zuwa asusunta. Daga nan ya koma kashe £98,000 duk wata.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng