Kasashenmu suna da tsohon tarihin zumunci, Buhari ya taya shugaban kasan Ghana murnar zarcewa

Kasashenmu suna da tsohon tarihin zumunci, Buhari ya taya shugaban kasan Ghana murnar zarcewa

- Shugaba Muhammadu Buhari ya mika sakon taya murnarsa ga zababben shugaban kasar Ghana

- Buhari ya yi wa Nana Akufo-Addo, dan takara karkashin jam'iyyar NPP fatan samar da cigaba da zaman lafiya a kasar

- Ya kara da bai wa sauran 'yan takarar wadanda suka sha kaye, hakuri da fatan za su taru su kai cigaban kasar

Shugaba Muhammadu Buhari ya miki sakon taya murnarsa ga Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo bisa samun nasarar lashe zabe da yayi, The Cable ta wallafa.

Akufo-Addo, wanda ya tsaya takara karkashin jam'iyyar NPP, kuma ya samu kuri'u 6,730,430, inda ya kayar da babban abokin takararsa tsohon shugaban kasa John Mahama, kuma dan takara karkashin jam'iyyar NDC wanda ya samu kuri'u 6,214,899.

A wata takarda ta ranar Alhamis, wacce Garba Shehu, Kakakin shugaban kasa ya saki, ya ce Shugaba Buhari ya baiwa sauran 'yan takara hakuri, sannan ya shawarcesu da su fara sanya kasarsu a gaba, su kuma tabbatar da zaman lafiya.

Kasashenmu suna da tsohon tarihin zumunci, Buhari ya taya shugaban kasan Ghana murnar zarcewa
Kasashenmu suna da tsohon tarihin zumunci, Buhari ya taya shugaban kasan Ghana murnar zarcewa. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: 2023: PDP ta magantu a kan bai wa Jonathan tikitin takarar shugaban kasa

Ya kara da tunatar da su yadda Ghana da Najeriya suke da tarihi da al'adu makusanta. A cewar Shehu, Buhari yana jiran ganin abokan hamayyar zababben shugaban kasar sun samar da zaman lafiya, tsaro da kuma cigaba ga 'yan kasar da kuma ECOWAS gaba daya.

"Shugaba Buhari ya yi wa Shugaban kasa Akufo-Addo fatan samun nasara a sabuwar kujerarsa, zaman lafiya da cigaban kasar gaba daya," cewar Shehu.

KU KARANTA: Zukekiyar budurwa ta rasu ana sauran kwanaki kadan aurenta

A wani labari na daban, jam'iyyar PDP ta yi wa Buhari kaca-kaca a ranar Alhamis. Ta ce ya kasa tabuka komai cikin shekaru 5 da yake kan karagar mulki, The Punch ta wallafa.

Kamar yadda sakataren yada labaran PDP, Kola Ologbondiyan yace, Buhari bashi da abinda zai cewa 'yan majalisar tarayya, shiyasa ba zai iya amsa gayyatarsu ba.

A cewarsa, "Shugaban kasa a tsorace yake, bashi da abinda zai fada wa 'yan Najeriya a kan matsalar tsaro. Wannan yasa yake ta kame-kame, ya tsere yaki fuskantar 'yan majalisar. Ya kasa yin komai tun da ya hau mulki, ciki har da bayar da tsaro."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng