Da duminsa: Manyan hafsoshin soji 18 sun harbu da cutar korona

Da duminsa: Manyan hafsoshin soji 18 sun harbu da cutar korona

- An gwada manyan hafsoshin sojin Najeriya, inda aka gano suna dauke da cutar COVID-19

- An gano hakan ne bayan sun koma daga wani taron sojoji na shekarar 2020 da aka yi Abuja

- Tuni NCDC ta umarci sauran sojojin da suka je taron, da iyalansu a kan su killace kansu na mako daya

An gwada a kalla manyan hafsoshin sojin Najeriya masu mukamin janar guda 18 kuma aka gano suna dauke da cutar COVID-19, Channels TV ta wallafa.

Ana zargin jami'an sojin sun yi cudanya da marigayi Manjo Janar Olu Irefin, wanda ya mutu sakamakon cutar COVID-19 makon da ya gabata.

Kamar yadda wata majiya ta tabbatar, wadanda aka gano suna dauke da cutar sun je taro shugabannin soji na shekarar 2020 da aka yi a wata cibiya a Abuja.

KU KARANTA: Yajin aiki: Mun cika wa ASUU dukkan alkawurran da muka dauka, FG

Da duminsa: Manyan hafsoshin soji 18 sun harbu da cutar korona
Da duminsa: Manyan hafsoshin soji 18 sun harbu da cutar korona. Hoto daga @ChannelsTV
Source: Twitter

Baya ga nan, an samu labarin yadda marigayi janar Irefin ya kaiwa abokan aikinsa ziyara kafin su je taron.

A don haka, NCDC ta umarci sauran sojojin da suka halarci taron da kuma iyalansu da su kebe kawunansu na mako guda.

Gidan talabijin din Channels sun bayyana yadda aka tabbatar an fesa magungunan da za su kashe kwayoyin cutar a dakin taron a kwanakin karshen mako.

Dama janar Irefin ya fara ciwo ne a makon da ya gabata a wani taron sojoji da suka yi, wanda daga nan aka kai shi asibiti.

Daga baya aka gano yana dauke da cutar COVID-19, ana cikin kulawa da lafiyarsa ya mutu.

KU KARANTA: Hadimin Buhari ya goyi bayan Zulum da dalilai, ya ce Borno ta samu cigaban tsaro

A wani labari na daban, a kan taron APC NEC, gwamnonin jam'iyya mai mulki sun yi wani taro a ranar Litinin da yamma, inda suka tattauna a kan makasudin taron da za a yi na NEC.

A taron, Premium Times ta gano cewa gwamnonin sun hada kai a kan hana shugaban kasa Muhammadu Buhari zaunawa da 'yan majalisar tarayya a kan batun rashin tsaron da ke kasar nan.

Sun ce hakan zai iya janyo wa shugaban kasa raini, ta yadda 'yan majalisar tarayya za su dinga kiransa taro a kan kananun abubuwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel