Sakon Bidiyo: A karo na biyu; El-Rufa'i ya sake killace kansa saboda annobar korona

Sakon Bidiyo: A karo na biyu; El-Rufa'i ya sake killace kansa saboda annobar korona

- Alkaluma da ke fitowa kwanakin baya bayan nan na nuna hauhawar adadin 'yan Nigeria da ke kamuwa da cutar korona

- A cikin makon nan ne gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i, ya sanar da cewa zai sake saka dokar kulle idan jama'a ba su kiyaye, sun bi doka ba

- El-Rufa'i, a cikin wani sakon bidiyo da ya wallafa a daren ranar Juma'a, ya sanar da cewa ya killace kansa

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i, ya sanar da cewa ya sake killace kansa bayan wasu na hannun damarsa da hadimansa sun kamu da kwayar cutar korona, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na tuwita.

El-Rufa'i ya sanar da hakan ne a wani sakon faifan bidiyo da ya wallafa a daren ranar Juma'a.

A cewarsa, ya killace kansa ne biyo bayan samun rahoton cewa wasu na hannun damarsa da makusanta iyalinsa sun kamu da kwayar cutar korona, kuma sun yi cudanya kafin fitowar sakamakon gwajinsu.

A ranar Alhamis ne El-Rufa'i ya ce akwai yiwuwar zai sake saka dokar kulle saboda hauhawar alkaluman masu kamuwa da cutar korona da ake samu a jihar da fadin kasa.

KARANTA: Kotun ICC za ta fara binciken hukumomin tsaron Nigeria

Abdallah Yunus Abdallah, mai taimakawa El-Rufa'i a bangaren watsa labarai, ya ce gwamnati za ta dauki wannan mataki ne saboda kare hakkin kare rayukan mutanen jihar ya rataya ne a wuyan gwamnan.

Sakon Bidiyo: A karo na biyu; El-Rufa'i ya sake killace kansa saboda annobar korona
Sakon Bidiyo: A karo na biyu; El-Rufa'i ya sake killace kansa saboda annobar korona
Source: UGC

A cewarsa, gwamnan ya yi wannan jan kunnen ne saboda alhakinsa ne ya kula da lafiyar mutanen jihar Kaduna, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

KARANTA: Ka sake nazari a kan tsige Nasiru Argungu; Sanatoci sun shawarci Buhari

Hadimin gwamnan ya kara da cewa babu abinda zai hana gwamnan Kaduna ya sake saka dokar kullen jama'a matukar basu kiyaye sharudan kare kai domin dakile yaduwar cutar ba ko kuma idan alkaluman masu kamuwa da cutar suka cigaba da hauhawa.

"Yaki da cutar korona aiki ne da ya rataya a wuyan dukan jama'a, ba iya gwamnati kadai ba, a saboda haka ya zama wajibi a kan mutane su kula tare da yin biyayya ga dokoki da matakan kare kai domin dakile yaduwar cutar," a cewarsa.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, zai shiga killace kansa, bayan daya daga cikin hadimansa na jiki ya kamu da cutar Korona ranar Alhamis.

Za'a yiwa gwamna Sanwo-Olu da mambobin majalisarsa gwajin cutar Korona ranar Juma'a amma zai cigaba da killace kansa kar lokacin da sakamakon ya fito.

Da yiwuwan cutar Korona ta dawo kwashe mutane yayinda mutane 3000 suka kamu cikin watan Disamba.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel