Kotun ICC za ta fara binciken hukumomin tsaron Nigeria
- Kotun ICC mai tuhumar manyan laifukan ta'addanci da cin zarafin jama'a ta ce za ta binciki hukumomin tsaron Nigeria
- Mai gurfanarwa a kotun ta ce ofshinta ya na kwararan hujjoji na zahiri da za'a iya kimantasu a kan jami'an hukumomin tsaron Nigeria
- Fatou Bensouda, mai gurfanarwa da ke shirin barin gado, ta lissafa wasu manyan laifuka da ICC ke zargin jami'an tsaron da aikatawa
Babbar mai gurfanarwa a kotun ICC ta bayyana cewa kotunsu a shirye ta ke domin fara binciken hukumomin tsaron Nigeria a kan laifukan da suka shafi ''cin zarafin al'umma'' da saba ka'idojin yaki, kamar yadda TheCable ta rawaito.
ICC kotu ce ta kasa da kasa da ke tuhumar manyan laifukan ta'addanci da cin zarafin jama'a. Hedikwatarta ta na kasar Switzerland.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da zarge-zarge suka yi yawa a kan cewa jami'an hukumomin tsaro a yankin arewa maso gabas da sauran sassan Nigeria suna cin zarafin fararen hula.
KARANTA: Kaduna: El-Rufa'i zai sake saka dokar kulle sakamakon hauhawar alkaluman korona
TheCable ta rawaito cewa takardar da ta kunshi bayanin ba ta bayar da takamaiman zargi ko zarge-zargen da kotun za ta bincika ba, sai dai, ta bayyana cewa "akwai isassun hujjojin da ICC za ta gudanar da bincike akansu."
Ofishin mai gurfanarwar ya ce ICC ta gudanar da bincike a gurguje tare da nazarin wasu zarge-zarge da suka shafi kisan dumbin jama'a, cin zarafi da keta haddinsu tare da kyararsu.
KARANTA: PANDEF: Muna son jin amsoshin tambayoyinmu uku daga bakin Buhari
Fatou Bensouda, mai gurfanarwa a kotun ICC, ta ce "akwai kwararan hujjoji da ke nuna cewa jami'an hukumomin tsaron Nigeria (NSF) sun aikata wadannan laifukan cin zarafin jama'a da laifukan da suka shafi yaki.
"Laifukan sun hada da kisa, azabtarwa, cin zarafin mata, kai hari a kan daidaiku da gungun fararen hula, daukan yara 'yan kasa da shekaru 15 aiki da sauransu."
Ta kara da cewa "akwai kwararan hujjoji da ofishina keda su, hujjoji na zahiri da za'a iya kimantasu. Ofishina zai samar da karin bayanai a taron shekara da zamu yi nan bada dadewa ba."
Legit.ng Hausa ta rawaito Farfesa Babagana Umara Zulum na cewa tsaro ya karu a jiharsa, Borno, da arewa ma so gabas a karkashin mulkin Buhari.
A cewar gwamnan, shaidu a kasa sun nuna cewa al'amuran harkokin rayuwa sun fara dawowa a kananan hukumomin da jama'a suka kauracewa a baya, kafin Buhari ya hau mulki.
Zulum ya bayyana hakan ne yayin da kungiyar dattijan arewa suka ziyarce shi domin yi masa ta'aziyyar kisan manoma 43 da 'yan Boko Haram su ka yi.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng