Ka sake nazari a kan tsige Nasiru Argungu; Sanatoci sun shawarci Buhari

Ka sake nazari a kan tsige Nasiru Argungu; Sanatoci sun shawarci Buhari

- Garba Shehu, a ranar Laraba, ya sanar da cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya sallami Nasiru Argungu daga mukaminsa

- Argungu ne babban daraktan ma'aikatar samar da guraben ayyuka ga 'yan kasa (NDE)

- Sai dai, majalisar dattijai ta ce akwai bukatar ya sake duba umarnin da ya bayar na tsige Argungu daga mukaminsa

Sanatoci a ranar Alhamis sun shawarci shugaban ƙasa, Muhammad Buhari, da ya sake duba ga umarnin da ya bayar na tsige Nasiru Argungun daga matsayinsa na babban daraktan ma'aikatar ɗaukar ayyuka (NDE).

Sanatocin sun faɗi aniyar tasu ne bayan wani sanata mai wakiltar Gabashin Jigawa, Ibrahim Hassan Haɗejia, ya tayar da maganar a zauren majalisar dattijai, kamar yadda Channels ta wallafa.

Majalisar dattijan ta dage akan cewa sauke Nasiru Argungu na iya kawo cikas tare da ɓata lokaci a tsarin ɗaukar gwamnatin tarayya wanda za'a ɗauki ma'aikata 774,000 a fadin Nigeria.

KARANTA: A Villa ake iskanci na gaske kuma Buhari ne jagora; Aisha ta yi martani kan gargadin shugaban kasa

Ka sake nazari a kan tsige Nasiru Argungu; Sanatoci sun shawarci Buhari
Ka sake nazari a kan tsige Nasiru Argungu; Sanatoci sun shawarci Buhari
Source: Facebook

Shugaba Buhari ya sauke Argungun daga kan muƙaminsa a matsayin shugaban hukumar ɗaukar ma'aikata(NDE) ranar Laraba.

KARANTA: Zanga-zanga: Buhari ya koka da kafafen yada labarai na ketare, ya ambaci sunayen biyu daga cikinsu

Babban mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Garba Shehu, shine ya bayyana umarnin Shugaban ƙasa na sauke Argungun daga ranar Juma'a, amma saukewar ta fara aiki ne daga ranar Litinin 7 ga watan Disamba.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa kwamitin shirye shirye da gudanarwar jam'iyyar APC ya sanar da ɗage shirinta na rijista da sake tantance ƴan jam'iyya wanda aka tsara gudanarwa ranar Asabar, 12 ga watan Disamba.

Yanzu za'a gudanar da rijistar a sati na biyu a cikin watan Junairun sabuwar shekara mai zuwa, 2021.

Sai dai jam'iyyar ta yi shiru akan takaimaimen kwanan watan da za'a gudanar da rijistar.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel