Yanzu yanzu: Buhari ya tafi Daura ziyara

Yanzu yanzu: Buhari ya tafi Daura ziyara

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi gida Daura, jihar Katsina domin ziyara ta mako daya

- Jirgin shugaban kasa ta isa Katsina misalin karfe 4.45 na yammacin ranar Juma'a 11 ga watan Disambar 2020

- Gwamna Aminu Bello Masari, mataimakinsa, Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar na daga cikin tawagar da ta tarbi shugaban kasar

A yau Juma'a 11 ga watan Disamba Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi gida garin Daura ta jihar Katsina domin kai ziyara.

Kakakin shugaban kasa Garba Shehu ya sanar da cewa jirgin shugaban kasar mai saukar ungulu ta sauka a Katsina a ranar Juma'a don ziyarar mako daya.

Yanzu yanzu: Buhari ya tafi Daura ziyara
Yanzu yanzu: Buhari ya tafi Daura ziyara. Hoto: @BashirAhmaad
Source: Twitter

Yanzu yanzu: Buhari ya tafi Daura ziyara
Yanzu yanzu: Buhari ya tafi Daura ziyara. Hoto: @BashirAhmaad
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Zahra Buhari ta taya mijinta murnar zagayowar ranar haihuwarsa da kalaman soyayya

Jirgin da ke dauke da shugaban kasar ya dira a filin tashin jirage na Musa Umaru Yaradua da ke Katsina misalin karfe 4.45 na yammacin ranar Juma'a inda gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina da mataimakinsa da wasu shugabannin hukumomi suka tarbe shi.

Har wa yau cikin tawagar da ta tarbi shugaban kasar akwai mai marataba sarkin Daura Alhaji Umar Faruk Umar da sauran 'yan majalisun masarautar jihar tare da kayatattun dawakai da fadawa

Jim kadan bayan saukarsa, Sarkin Daura ya bawa shugaban kasa kyuatar doki da takobi da aka kawata shi a matsayinsa na Bayajiddan Daura.

KU KARANTA: Zahra Buhari ta taya mijinta murnar zagayowar ranar haihuwarsa da kalaman soyayya

Yayin da ya ke Daura, shugaban kasar zai gana da mutane daban daban da suka shafi 'yan uwa da sauran na kusa da shi amma zai halarci taron FEC a ranar Laraba ta fasahar bidiyo da sauti na intanet wadda mataimakinsa Yemi Osinbajo zai jagoranta.

Rabon shugaba Buhari da zuwa Daura sun watan Disambar bara saboda dalilan annobar korona da ta takaita zirga-zirga a kasashen duniya ciki har da Najeriya.

A wani labarin, rundunar sojojin ruwan Najeriya ta fitar da wani sanawar dauke da hotuna da sunayen wasu jami'anta da suka tsere daga aiki tana mai neman duk wanda ke da bayani da zai taimaka a kamo su ya tuntubi ofishinta ko na 'yan sanda mafi kusa.

The Punch ta ruwaito cewa an wallafa sanarwar ne a hedkwatar rundunar sojin ruwan da ke binrin tarayya Abuja. Rundunar soji tana neman jami'anta 43 ruwa a jallo.

Sanarwar ta kuma wajabtawa dukkan jami'an rundunar da ke da bayannan game da jami'an da suka tsere su kamo su 'idan ba haka ba a dauke su a matsayin wadanda suke taimaka musu'.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel