Tallafin Covid-19: An gane mahaifina ba shine matsalar Najeriya ba - Zahra Buhari
- A 'yan kwanakin da suka gabata ne 'yan Najeriya suka gano ma'adanar kayan tallafin COVID-19, kuma suka shiga suka kwashe kayan abincin tas
- Hakan ya kawo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani, wanda har wata mai shirya fina-finai, Mansurah Isah ta yi wata wallafa a Instagram
- Tace ga dukkan alamu, shugaba Buhari ba matsalar Najeriya bane, tunda ya bayar da kayan abinci, rabawa ne ba a yi ba, Zarah Buhari ta kara wallafa wannan wallafar ta Mansurah
Kwanaki kadan da suka gabata, 'yan Najeriya sun gano ma'adanar da aka killace kayan abincin tallafin COVID-19 wanda CACOVID suka bayar, kuma sun fada gidajen sun kwashesu tas.
Kayan tallafin sun hada da kayan abinci iri-iri wadanda ya kamata a rabawa talakawan Najeriya.
'Yan Najeriya da dama sun yi ta caccakar gwamnatin jihohi a kan rashin raba kayan abinci da ya kamata su yi lokacin da aka shiga tsanani.
KU KARANTA: ICPC ta gurfanar da dan majalisar tarayya a kan karbar cin hanci daga 'yan kwangila
KU KARANTA: Da duminsa: Jami'an tsaro sun isa fursuna ta Ikoyi bayan yunkurin balle ta
Wata mai shirya fina-finai, Mansurah Isah, ta wallafa a shafinta na Instagram, inda ta nuna yadda aka gano kayan tallafin, wanda hakan ke nuna ba shugaban kasa ne matsalar Najeriya ba.
Zarah Buhari-Indimi, wacce diya ce ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta kara wallafa wallafar Mansurah a shafinta na Instagram, da alamu ta yadda da abinda Mansurah Isah ta wallafa.
A wani labari na daban, zanga-zangar EndSARS ta canja salo cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, jaridar The Nation ta wallafa.
A jawabin da shugaban kasa yayi da daren Alhamis, wanda ya ja kunnen wadanda suka yi uwa da makarbiya a kan zanga-zangar ya ce lallai gwamnatin tarayya ba za ta yarda da sauran ta'addanci ba.
Yace: "Wajibi ne in ja kunnen wadanda suka canja wa zanga-zangar EndSARS salo daga asalin makasudinta, wadda matasa suka fara a kan dakatar da rundunar SARS.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng