Zanga-zanga: Buhari ya koka da kafafen yada labarai na yamma, musamman BBC da CNN

Zanga-zanga: Buhari ya koka da kafafen yada labarai na yamma, musamman BBC da CNN

- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya koka da halayyar wasu kafafen yada labarai na kasashen ketare

- Buhari ya zargi kafafen yada labaran da jirgewa bangare guda a rahotannin da suka yada dangane da zanga-zangar EndSARS

- Gidan talabijin na CNN ya wallafa wani faifan bidiyo da ke nuna cewa dakarun soji sun budewa fararen hula a Lekki, Legas

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya koka da halayyar wasu kafafen yada labari na kasashen ketare a kan yadda suka yada labaran da suka shafi zanga-zangar EndSARS.

A cikin wani takaitaccen sako da shugaba Buhari ya wallafa a shafinsa na tuwita, ya ce kafafen yada labarai na ketare, musamman CNN da BBC sun jirge bangare guda wajen yada labaran da suka shafi zanga-zangar.

Zanga-zanga: Buhari ya koka da kafafen yada labarai na yamma, musamman BBC da CNN
Zanga-zanga: Buhari ya koka da kafafen yada labarai na yamma, musamman BBC da CNN @Buhari Sallau
Asali: Facebook

Wasu kafafen yada labarai na ketare sun wallafa rahotannin cewa dakarun soji sun budewa fararen hula wuta yayin zanga-zangar EndSARS, musammam a yankin Lekki da ke jihar Legas.

KARANTA: Kungiyar Malaman Kano ta magantu a kan batun goyon bayan takarar Tinubu a 2023

Sai dai, gwamnatin tarayya, tun a wancan lokacin, ta musanta zargin cewa jami'an tsaro sun kashe fararen hula.

Hasali ma, gwamnati ta ce ita aka yi wa barna, saboda an kashe 'yan sanda tare da kona ofisoshinsu da gidan yari duk da sunan zanga-zanga.

KARANTA: Mayakan ISWAP sun kashe sojoji 10 tare da yin garkuwa da guda ɗaya a jihar Borno

A cewar shugaba Buhari, "dole a fadi cewa kafafen yada labarai na ketare ba su yi adalci ba a labaran da suka yada yayin zanga-zangar ENDSARS, musamman daga CNN da BBC. Ban ji dadin labaran da su ka yada ba, wanda ko kadan bai ambaci cewa an kashe jami'an 'yan sanda ba, an kona caji ofis, an balle gidajen yari".

Legit.ng ta rawaito cewa Aisha Yesufu, 'yar gwagwarmaya kuma jagorar zanga-zangar EndSARS, ta mayar da martani mai yaji ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

A ranar Litinin ne shugaba Buhari ya yi gargadin cewa zai magance duk wani salo na iskanci kuma ta kowacce siga aka bullo da shi yayin martani ga sake yunkurin dawo da zanga-zangar ENDSARS.

A martanin da ta yi akan gargadin shugaba Buhari, Aisha ta ce a fadar shugaban kasa ake iskanci na gaske.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng