APC ta ɗage ranar fara rijista da tantance mambobin jam'iyyarta
- Jam'iyyar APC ta sanar da dage fara rijistar sabbi da tantance soffin mambobinta
- Karshen watan Nuwamba ne APC ta sanar da cewa za ta fara aikin rijistar daga ranar 12 ga watan Disamba
Kwamitin shirye shirye da gudanarwar jam'iyyar APC ta ɗage shirinta na rijista da sake tantance ƴan jam'iyya wanda aka tsara gudanarwa ranar Asabar, 12 ga watan Disamba.
Yanzu za'a gudanar da rijistar a sati na biyu na watan Junairun shekarar 2021, kamar yadda Leadership ta rawaito.
Sai dai jam'iyyar ta yi shiru akan takaimaimen kwanan watan da za'a gudanar da rijistar.
Duba da gabatowar shagulgulan bikin Kirismeti, mai kula da kwamitin ya ce wannan zai bawa Kiristoci damar yin shagulgulan bukukuwan Kirismeti tare da bawa jam'iyyar damar kammala shirye shiryen yin rijistar.
A baya, kwamitin kula da tsare - tsare na jam'iyyar APC ya ce sun ce sun kammala duk shirye-shirye don fara aiwatar da sabuwar rijista da sabunta rijistar ƴan jam'iyya daga ranar 12 ga watan Disamba.
Shugaban kwamitin, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ne ya fadi hakan a sanarwar da suka fitar a birnin tarayya, Abuja, ranar Litinin bayan ganawa da masu ruwa da tsaki, wanda suka haɗa da Shugaba Muhammad Buhari.
Ya ce za'a fara rijistar shaidar zama ɗan jam'iyya daga ranar Asabar, 12 ga Disamba, 2020 zuwa Asabar, 9 ga watan Junairu, 2021.
A kwanakin baya ne Legit.ng Hausa ta rawaito Buni na cewa nan bada dadewa ba jam'iyyar APC za ta tashi wata guguwar siyasa da za ta girgiza Najeriya.
Buni ya bayyana hakan ne bayan gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi da Sanata Elisha Abbo daga jihar Adamawa sun sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Shugabanni da jagororin jam'iyyar APC sun gana a sirrance da tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng