Boko Haram: Dakarun Najeriya na daya daga cikin zakakuran soji a Afrika, Magashi
- Ministan tsaro, Manjo janar Bashir Magashi, ya ce sojojin Najeriya sune mafi nagarta a cikin Afirka
- Magashi ya ce rundunar sojin Najeriya za ta iya kawo karshen Boko haram a arewa maso gabas
- Ya ce har kasashen ketare irin Sierra Leone suka je kuma suka yi samu nasarori masu yawa
Ministan tsaro, Manjo janar Bashir Magashi, ya ce sojojin Najeriya suna daga cikin sojoji mafi nagarta a Afirka. Ya fadi hakan ne a ranar Alhamis, inda yace suna da damar kawo karshen duk wani makiyi idan aka ba su damar yin hakan.
A cewar Magashi, rundunar soji za ta iya kawo karshen Boko Haram a arewa maso gabas, saboda sun ci nasara a yakin da suka je cikin wasu kasashen ketare.
A cewarsa, "A Afirka, ya kamata sojojin Najeriya su zama na daya a kwazo, saboda mun dade muna samun nasarori har a kasashen ketare. Mun je ECOMOG, mun yi iyakar kokarinmu. Mun je Sierra Leone, mun ci nasara. Amma sakamakon dadewar wannan yakin, mutane har sun gaji.
KU KARANTA: Lawan: 'Yan majalisar dattawa ba kansu suke wa aiki ba, Ahmad Lawan
"Yan Boko Haram ba sa tsayawa wuri daya, da zarar sun kai farmaki wani wuri sai su gudu su koma wani wurin. Matsalar kawai ba mu san inda suke zama bane. Yanzu kuwa da muka gano su, gashi nan rundunar sojin sama da ta kasa suna karar da su."
Magashi ya fadi hakan ne a wata tattaunawa da gidan Talabijin na Channels sukayi dashi, wanda The Punch ta kula dashi yau.
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace basarake, sun hada da mutum 12 a Katsina
A wani labari na daban, a taron da shugaba Buhari yayi da gwamnoni, ya zauna tsaf ya saurari korafi daga yankuna 6 da ke kasar nan, daga bakin gwamnoni, a kan harkokin tsaro da ke addabar kasarnan.
Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Garba Shehu yace, shugaban kasa ya ce, "Wajibi ne gwamnati tayi aiki tare da shugabannin gargajiya. Ya kamata a hada kai dasu don a san ta inda za a bullo wa lamarin."
Buhari ya ce mulkinsa ya yi kokarin gyara yankunan arewa maso gabas da kudu-kudu, amma yankin kudu-kudu suna cikin mawuyacin hali, Daily Trust ta wallafa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng