Ba mu gayyaci Buhari don kure shi ba, Kakakin majalisar wakilai
- Majalisar tarayya ta ce bata gayyaci Buhari don ta kure shi ba
- Ta so su tattauna ne a kan matsalolin tsaro da ke damun Najeriya
- Ta kara da cewa mafi yawan 'yan majalisar 'yan jam'iyyarsa ne
A ranar 1 ga watan Disamba, majalisar tarayya ta gayyaci Buhari don tattaunawa a kan harkokin tsaro, bayan 'yan Boko Haram sun kashe wasu manoman shinkafa a jihar Borno.
Gayyatar da majalisar ta yi wa Shugaban kasa ta janyo cece-kuce iri-iri, saboda wasu daga cikin 'yan majalisar sun wajabta wa Buhari amsa gayyatar.
A ranar 4 ga watan Disamba, Femi Gbajamiala, kakakin majalisar ya bayyana cewa Buhari ya amince da zama da majalisar.
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace basarake, sun hada da mutum 12 a Katsina
Murna ta koma ciki ne a ranar Laraba, bayan Abubakar Malami, Antoni janar na gwamnatin tarayya, ya ce majalisar tarayya ba ta da hurumin gayyatar shugaban kasa a kan ayyukan jami'an tsaronsa.
Kakakin majalisar, ya ce Shugaban kasa bai fi karfin jam'iyya ba, tunda mafi yawan 'yan majalisar 'yan jam'iyyar APC ne.
Kalu ya fadi hakan ne a ranar Alhamis a Abuja, inda yace majalisar ta bukaci zaunawa da shi don tattaunawa a kan matsalolin tsaro da ke addabar Najeriya.
KU KARANTA: Boko Haram: Gwamnatin Yobe ta dauka alwashin ba wa jami'an tsaro tallafin kayan aiki
A wani labari na daban, Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya ce 'yan majalisar dattawa ba kansu suke yi wa aiki ba, jaridar The Cable ta wallafa.
Yayin da Lawan yake jawabi a wani taro a majalisar ranar Laraba, ya ce 'yan majalisar dattawa suna sane da abubuwan da suke yi.
A cewarsa, 'yan majalisar sune wadanda suka fi saukin zuwa garesu cikin wadanda aka zaba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng