Zukekiyar budurwa ta rasu ana sauran kwanaki kadan aurenta

Zukekiyar budurwa ta rasu ana sauran kwanaki kadan aurenta

- Wata budurwa mai shekaru 31 ta rasu ana saura kwanaki kadan bikinta

- Juliet ta gama sanar da 'yan uwa da abokan arziki cewa ta kusa zama amarya

- Kwatsam sai mutuwa da sunkuce ta bayan ta yi gajeriyan rashin lafiya

Wata budurwa mai shekaru 31 ta rasu ana saura kwanaki kadan aurenta a jihar Imo, shafin Linda Ikeji ya tabbatar.

Budurwar mai suna Juliet Nlemadim ta rasu a ranar 3 ga watan Disamba bayan wata kwarya-kwaryar rashin lafiya da tayi. Zaa yi jana'izarta a kauyensu, Uborji Okuku, Owerri ta yamma a ranar Juma'a, 11 ga watan Disamban 2020.

Kamar yadda bayanai suka kammala, matar wacce ta gama jami'ar jihar Legas tana shirin zama amaryar Nnaemeka Abakporo a ranar Laraba, 30 ga watan Disamba, ashe mutuwa tana tafe.

Zukekiyar budurwa ta rasu ana sauran kwanaki kadan aurenta
Zukekiyar budurwa ta rasu ana sauran kwanaki kadan aurenta. Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

KU KARANTA: 2020: Fitattu 8 a Najeriya da suka siya wa iyayensu motoci da gidaje

Tuni 'yan uwa da abokan arzikinta suka fara wallafa mutuwar a shafukansu na kafafen sada zumuntar zamani.

Wani Achor Goddey ya wallafa a shafinsa na Facebook:

"Juliet Nlemadim! Ina jin radadin wallafar nan da zan yi, amma haka nan zan yi cikin hawaye da takaici.

"Makon da ya gabata kika sanar da ni labarin aurenki, kika ce ana shirin yin shi a ranar 30 ga watan Disamba, kuma na yi miki alkawarin zama daya daga cikin wadanda za su taya ki farinciki da shagali a ranar.

"Ba mus an mutuwa za ta yi gaggawar daukeki ba, sai dai mu ce sai watarana, sai mun hadu a gidan gaskiya."

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace basarake, sun hada da mutum 12 a Katsina

A wani labari na daban, An kama wani direban mota, Fred Onwuche, saboda amfani da tabarya wurin ji wa wani jami'in LASTMA ciwo a Kosoko Rasak, wuraran Jakande a Lekki jihar Legas.

Al'amarin ya faru ne a ranar Talata, 8 ga watan Disamba kamar yadda wata takarda daga ofishin shugaban LASTMA, Olajide Oduyoye ta sanar. Ta tabbatar da yadda jami'in ya tsayar da direban saboda karya doka yayin tuki.

Hakan ya fusata Onwenche, inda yayi gaggawar dakko tabarya ya buga wa kan jami'in LASTMA a kai, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel