APC ta janye daga zaben maye gurbi da za'a kammala a Zamfara

APC ta janye daga zaben maye gurbi da za'a kammala a Zamfara

- A Ranar Asabar, 6 ga watan Disamba, INEC ta gudanar da sauran zabukan maye gurbi a fadin Nigeria

- INEC ta bayyana zaben kujerar majalisar dokoki na mazabar Bakura a matsayin wanda bai kammalu ba

- Sai dai, tun kafin INEC ta sanar da sabuwar ranar kammala zaben, jam'iyyar APC ta ce ta janye

Jam'iyyar PDP reshen jihar Zamfara ta bayyana matukar mamaki da kaduwarta da samun labarin cewa jam'iyyar APC ta janye daga zaben maye gurbi da za'a kammala a mazabar Bakura, kamar yadda Channels ta rawaito.

A ranar Lahadi ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar da cewa zaben kujerar dan majalisar jiha na mazabar Bakura bai kammalu ba bayan soke sakamakon wasu mazabu biyar.

Sai dai, tun kafin INEC ta sanar da sabuwar ranar sake gudanar da zabe, jam'iyyar APC ta ce ba zata shiga zaben da za'a kammala ba, ta fice daga takarar neman kujerar.

KARANTA: Gani Adams: Ni da Obasanjo haihata-haihata, ba zamu taba sulhuntawa ba

A cikin jawabin da shugaban jam'iyyar PDP na jihar Zamfara, Tukur Danfulani, ya fitar ranar Talata, yace janyewar APC ba ta basu wani mamaki mai yawa ba.

APC ta janye daga zaben maye gurbi da za'a kammala a Zamfara
APC ta janye daga zaben maye gurbi da za'a kammala a Zamfara
Source: UGC

Ya bayyana cewa jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Zamfara ta yi farin ciki saboda APC ba ta zarge ta da aikata wani mugun abu ba a jawabin janyewa da ta fitar.

KARANTA: ISWAP ta kashe sojoji 10 tare da yin garkuwa da guda ɗaya a jihar Borno

"Kiranmu har yanzu shine hukumomin tsaro su tabbatar da cewa sun bawa jama'a tsaro kafin da kuma lokacin zabe da bayan kammala zaben. Kar su bari batagari su samu damar kawo hargitsi da rudani," a cewar Danfulani.

A cewar shugaban na PDP, APC ta janye daga takarar ne saboda tsoron cewa za ta sha kaye tunda tun kafin a sanar da daga zaben, PDP ce a gaba kafin a bayyana zaben a matsayin wanda bai kammalu ba.

A ranar Talata ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa ma'aikatan wucin gadi guda biyu da suka bace yayin zaben maye gurbi na ranar Asabar a jihar Zamfara sun bayyana.

An samu matsalar satar akwatin zabe da barkewar rikici a mazabar 001 da ke karamar hukumar Bakura yayin zaben maye gurbin.

Yayin da take gabatar da sakamakon mazabar, wakiliyar INEC mai kula da mazabar, A'isha Bawa, ta ce ta nemi ma'aikatan Sama ko kasa, ba ta gansu ba, sun bace bat bayan barkewar rikici.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel