Shugaba Buhari ya nada Abubakar Fikpo a matsayin mukaddashin shugaban hukumar NDE

Shugaba Buhari ya nada Abubakar Fikpo a matsayin mukaddashin shugaban hukumar NDE

- Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta nada Abubakar Fikpo a matsayin mukaddashin Shugaban hukumar NDE

- Gwamnatin tarayya ce ta sallami Nasir Argungu, wanda ya kasance rike da mukamin daga kan kujerarsa

- Fikpo ya kasance darakta mafi girma a NDE bayan ficewar tsohon Darakta Janar na hukumar

Gwamnatin tarayya ta nada Abubakar Fikpo a matsayin mukaddashin darakta janar na hukumar daukan ma’aikata, domin ya maye gurbin Dr Nasiru Argungu wanda aka dakatar daga matsayin a ranar 7 ga watan Disamba.

Festus Keyamo, karamin ministan kwadago da aikin yi, ya tabbatar da nadin a wata wasika mai taken “nada ka a matsayin mukaddashin darakta janar na hukumar daukan ma’aikata."

An kuma aika wasikar zuwa ga Fikpo a ranar Laraba, 9 ga watan Disamba, a Abuja, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Shugaba Buhari ya nada Abubakar Fikpo a matsayin mukaddashin shugaban hukumar NDE
Shugaba Buhari ya nada Abubakar Fikpo a matsayin mukaddashin shugaban hukumar NDE Hoto: @GarShehu
Asali: Twitter

“Biyo bayan umurni daga Shugaban kasa na saukewa Dr Nasiru Argungu nauyi a matsayin Darakta Janar na hukumar NDE, don haka ana umurtanka da ka ci gaba a matsayin mukaddashin darakta janar na hukumar har zuwa lokacin da Shugaban kasar zai tabbatar da nadin.

“Wannan ya kasance ne don tabbatar da ganin babu gibi a gudanarwar hukumar,” in ji ministan.

KU KARANTA KUMA: Kyari da manyan yan siyasa 9 da suka mutu a 2020 (jerin sunaye)

Mista Keyamo, wanda ya kuma kasance minista mai sanya ido a hukumar, ya ce umurnin ya fara aiki daga ranar 7 ga watan Disamba.

Ministan ya bukaci mukaddashin darakta janar din a kan ya tabbatar da gudanarwa yadda ya kamata a hukumar.

Sannan kuma ya umurce shi da ya tabbatar da Dr Nasiru Argungu ya mika masa dukkanin kayayyakin gwamnati da ke hannunsa yadda ya kamata.

A baya mun ji cewa, Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke shugaban hukumar daukan ma'aikata, Dakta Nasiru Mohammed Ladan Argungu daga mukaminsa.

Sanarwar saukewar na kunshe ne cikin wata wallafa da babban mataimakin shugaban kasa a bangaren watsa labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Talata.

KU KARANTA KUMA: Kakakin majalisar Bauchi ya ce baya shirin barin APC

Sanarwar ta ce Buhari ya umurci karamin ministan Kwadago da Ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ya nada shugaban riko daga cikin manyan direktocin hukumar don maye gurbin Argungu a yanzu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel