Jam'iyyar APC ta sanar da lokacin bayyana yankin da za ta ba wa tikitin takarar shugaban kasa

Jam'iyyar APC ta sanar da lokacin bayyana yankin da za ta ba wa tikitin takarar shugaban kasa

- Jam'iyyar APC ta kara wa Mai Mala Buni wa'adin mulkin kwamitin rikon kwarya na watanni 6

- Jam'iyyar ta sanar da cewa za ta fitar da yankin da shugaban kasa zai bayyana a watan Yunin 2021

- Hakan zai bada gyara duk wata baraka da jam'iyyar take fuskanta, da kuma yiwa sababbin 'yan jam'iyyar rijista

Jam'iyyar APC ce take da alhakin tsayar da dan takarar shugabancin kasa na watan Yunin 2023, kamar yadda majiya daga jam'iyyar ta tabbatar wa da Daily Trust a ranar Talata.

Majiyar ta ce idan har a arewa ta fitar da shugaban jam'iyya, kudu za a baiwa damar fitar da dan takarar shugaban kasa, ko kuma arewa ta fitar da dan takarar shugaban kasa, kudu ta fitar da shugaban jam'iyya.

A taron gaggawa da NEC tayi, ta kara wa Mai Mala Buni wa'adin cigaba da shugabancin kwamitin rikon kwaryar na watanni 6. Dama wa'adin shugabancinsa na kwamitin zai kare ne a ranar 25 ga watan Disamba, amma NEC ta kara wa'adin zuwa ranar 30 ga watan Yunin 2021.

Jam'iyyar APC ta sanar da lokacin bayyana yankin da za ta ba wa tikitin takarar shugaban kasa
Jam'iyyar APC ta sanar da lokacin bayyana yankin da za ta ba wa tikitin takarar shugaban kasa. Hoto daga @daily_trust
Source: Twitter

KU KARANTA: Budurwa ta kamu da korona, an daura aurenta da masoyanta sanye da kayan kariya

Cikin dalilan da jam'iyyar ta bayar shine za ta baiwa kwamitin damar karasa shigarwa da kuma rijistar sababbin 'yan jam'iyya, sannan hakan zai kara bai wa jam'iyyar damar karasa daidaita wasu lamurran cikinta.

"Wannan yana daya daga cikin dalilan da suka sanya shugaba Muhammadu Buhari cikin maganar da yayi a taron NEC ya sanya yace za a yi kokarin magance duk wasu matsalolin cikin jam'iyya da amincewa da maja tsakanin wasu jam'iyyu da APC," kamar yadda wata majiya ta sanar.

Ya ce batun yadda wani bangare daga jam'iyyar APC ne zai fitar da wanda zai tsaya takarar shugabancin kasa yana daya daga cikin abubuwan dake ci wa shugaba Buhari tuwo a kwarya.

Akwai kuma majiyar da take tunanin wasu masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC da ke arewa za su yi amfani da karfin ikonsu su rike mulkin a arewa, amma kuma 'yan kudu za su ga cewa an ci amanarsu, kuma ba a yi musu adalcin da sukayi wa arewa a 2015 ba.

KU KARANTA: Bayan kama budurwarsa tana cin amanarsa, saurayi ya bukaci shawara a kan abinda ya dace da ita

A wani labari na daban, wata mata ta maka saurayinta a kotu sakamakon bata mata lokaci duk da shekarunsu 8 tare amma ya gaza aurenta.

Ngoma ta sanar da wata kotu a Zambia cewa ta gaji da jiran Herbert Salaliki mai shekaru 28, wanda yayi mata alkawarin aure.

A cewar Mwebantu, har yanzu Ngoma tana zaune da iyayenta duk da ta haifa wa Herbert da guda daya, shi kuma yana zaman kansa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
APC
Online view pixel