Rashin tsaro: Abinda gwamnoni suka sanar da Buhari, Adesina

Rashin tsaro: Abinda gwamnoni suka sanar da Buhari, Adesina

- Taron da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi da gwamnonin jihohi 36, ya haifi da mai ido

- Shugaban kasa ya kara wa gwamnonin kwarin guiwa, sannan ya tabbatar da yadda zai basu gudunmawa

- Ya ce zai tabbatar ya sa an kara horar da sojoji da kuma kara musu makamai don yakar ta'addanci

Femi Adesina, mai ba wa shugaban kasa shawara na musamman a kan yada labarai, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar wa gwamnonin jihohi 36 cewa mulkinsa ya zage damtse wurin kawo karshen rashin tsaro a kasar nan.

A wani taro da aka yi a ranar Talata, 8 ga watan Disamba, gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum da takwarorinsa na jihohin arewa maso gabas basu tayar da zancen kawo wasu mayaka ba don kawar da 'yan ta'addan Boko Haram a yankinsu.

The Punch ta ruwaito yadda Zulum ya bayyana bukatunsa 6 ga gwamnatin tarayya don kawo karshen ta'addancin 'yan Boko Haram bayan kashe manoman shinkafa 43 da suka yi a Borno, watan da ya gabata.

Rashin tsaro: Abinda gwamnoni suka sanar da Buhari, Adesina
Rashin tsaro: Abinda gwamnoni suka sanar da Buhari, Adesina. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

KU KARANTA: Jama'a sun caccaki wani mutum da yace za a iya aure da albashin N30,000

Cikin bukatun da ya gabatar har da neman tallafin sojoji daga gwamnatin kasar Chadi, Kamaru da kuma Nijar, tare da wasu mayakan na daban don cin galaba a kan Boko Haram.

Bayan ganin yadda kashe-kashe suka tsananta a kasar nan, NGF, karkashin mulkin gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, sun yi taro da shugaban kasa a fadarsa.

Amma Kakakin shugaba kasa ya ce gwamnan jihar Borno da takwarorinsa daga arewa maso gabas ba su bayyana wata bukatarsu ta neman taimako daga kasashen ketare ba.

Adesina ya yi maganar ne a ranar Talata a gidan talabijin na Channels, wanda The Punch ta kula dashi.

KU KARANTA: Maryam Sanda: 'Yan sanda sun damke matar auren da ta halaka mijinta

A cewarsa, "Lallai taron ya yi amfani. Gwamnonin jihohi 36 duk sun hada kai, ba a maganar jam'iyya a lokacin.

"Bayan shugaban NGF, Kayode Fayemi ya yi magana, ya gayyaci duk wani gwamna don ya sanar da abubuwan da ke faruwa a yankinsa, dangane da tsaro."

Adesina yace duk gwamnonin sunyi magana akan rashin tsaron dake addabar yankinsu, musamman arewa maso yamma, arewa maso gabas, arewa ta tsakiya da sauransu.

A wani labari na daban, a jiya, ranar 6 ga watan Disamba ne rundunar Operation Whirl Stroke ta amsa kiran 'yan sa kai a kan wani hari da ake zargin wasu makiyaya na kauyen Tsehombe-Adaka suka kai.

Take a nan aka yi karon batta tsakanin 'yan ta'addan masu miyagun makamai da kuma jaruman sojojin.

Sojojin sun zagaye 'yan ta'addan, inda suka yi kaca-kace da su har suna kashe mutane 3 a cikinsu. Sauran kuma suka tsere da raunuka sakamakon harbin da suka sha.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel