Majalisa bata da ikon tilasta wa Buhari ya bayyana gabanta, in ji Malami
- Atoni janar na Najeriya, Abubakar Malami ya ce Majalisar Tarayya bata da ikon tilasta wa shugaban kasa gurfana gabanta
- Malami ya yi wannan jawabin ne kan gayyatar da majalisar wakilai ta yi wa Buhari kan taɓarbarewar tsaro
- Ana tsammanin shugaban kasar zai amsa kirar majalisar ranar Alhamis amma yanzu babu tabbas hakan zai faru
Abubakar Malami, Atoni Janar kuma ministan Shari'a na ƙasa ya ce a ƙarƙashin doka majalisa bata da ikon tilasta wa shugaba Muhammadu Buhari ya gurfana gabanta kamar yadda The Punch ta ruwaito.
A makon da ta gabata, majalisar wakilai na tarayya ta cimma matsayar gayyatar shugaban ƙasar don mata bayani kan taɓarbarewar tsaro a ƙasar a wani zama da tayi karkashin jagoracin kakakin majalisa Femi Gbajabiamila.
Malami, ya yi wannan jawabin ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba mai taken, 'Gayyatar Buhari: NASS tana daukan matakan da suka saba wa doka'.
Majalisar ta dauki wannan matakin ne bayan halaka manoma 43 da 'yan ta'adda suka yi a garin Zabarmari na jihar Borno.
DUBA WANNAN: ASUU ta amince za ta janye yajin aiki ranar 9 ga watan Disamba, inji Ngige
An shirya cewa shugaban zai gurfana gaban majalisar a ranar Alhamis amma yanzu babu tabbacin zai amsa kirar.
A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, Malami ya ce, "majalisar tarayya bata da iko ko karfin neman shugaban kasa ya gurfana gabanta a kan ayyukan dakarun sojoji".
Majalisar ta aike wa shugaba Muhammadu Buhari gayyatar ne don karin hare hare da ake samu na 'yan bindiga da 'yan ta'adda a kasar.
KU KARANTA: Dakatar da ni da jam'iyya ta yi ya saba doka, tsohon mataimakin shugaban APC, Eta
A wani labarin daban, kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC mai mulki a ranar Talata ya janye sharadin takara ga wanda suka shiga ko suke shirin shiga jam'iyyar.
Sharadin zai bada damar tsayawa takara a duk wata kujerar mulki ba tare da la'akari da dadewa a jam'iyyar ba.
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ne ya bayyana haka ga majalisa bayan kammala taron kwamitin kamar yada The Punch ta ruwaito.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng