Gani Adams: Ni da Obasanjo haihata-haihata, ba za mu taba yin sulhu ba

Gani Adams: Ni da Obasanjo haihata-haihata, ba za mu taba yin sulhu ba

- Bisa ga dukkan alamu ba za'a taba samun jituwa tsakanin Obasanjo da Gani Adams, tsohon shugaban OPC ba

- A lokacin mulkin Obasanjo ne aka kama Adams aka kulle bisa zarginsa da amfani da OPC wajen tayar da rikici

Iba Gani Adams, Aare Ona Kakanfo na ƙasar Yoruba, ya maida martani kan kalaman tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo,wanda ya ce Adams ya ɓata tsari da dokokin Obasanjo a baya, kamar yadda tvc ta rawaito.

Rahotanni daga gidajen jaridu a makon da ya gabata sun nuna cewa an yi zaman sulhu tsakanin Adams da Obasanjo a gidan fitaccen shugaban ƙungiyar zamantakewa da siyasa ta Yarbawa, Afenefere, Chief Ayo Adebanjo.

Adams,wanda shine shugaban gudanarwa na Oodua People Congress, ƴan sanda sun kama shi lokacin mulkin Obasanjo a shekarar 2001 bisa zargin tada tarzoma a wasu ɓangarorin ƙasar nan wanda ke da alaƙa da ƙungiyarsa.

KARANTA: ISWAP ta kashe sojoji 10 tare da yin garkuwa da guda ɗaya a jihar Borno

Amma Obasanjo a cikin wani jawabi da mai taimaka masa wajen yaɗa labarai, Kehinde Akinyemi, ya fitar bayan wata ganawa a ranar Laraba, ya ce bai halarci zaman sulhu a gidan Adebanjo, shi da Aare Ona Kakanfo, Iba Gani Adams, ba.

Gani Adams: Ni da Obasanjo haihata-haihata, ba za mu taba yin sulhu ba
Gani Adams: Ni da Obasanjo haihata-haihata, ba za mu taba yin sulhu ba @tvc
Asali: Twitter

Ya ce, "ban yi faɗa da Gani Adams ba, amma rayuwarsa ta baya ba tayi dai-dai da tsarin tafiyar da rayuwata ba.

"A baya, a gwamnatance da kuma kankin kaina na hana Adams ganina, na hana shi damar ziyarta ta."

"Idan har wani yana jin cewa ina faɗa da shi ko ita, kuma akwai buƙatar sulhuntawa, to ba makawa za'a yi sulhun ne a gidana da ke Abeokuta kaɗai."

Da yake maida martani a ganawa da ƴan jarida a ranar Laraba, Adams ya ce har yanzu bai gane abin da Obasanjo ke nufi da "rayuwarsa ta baya ba."

KARANTA: Gwamnatin tarayya ta na amfani fasahar Isra'ila wajen leken asirin wayoyin 'yan Nigeria

Ya ce "ban san me Baba Obasanjo ya ke nufi da rayuwata ta baya ba. Na yarda da shi kan cewa halin mu bai zo ɗaya ba saboda shi ɗin ba mai son cigaba bane."

"Obasanjo ba zai so halayyar duk wani ɗaɓ Najeriya mai cigaba ba."

"Ban taɓa buƙatar ganin Obasanjo a kowanne irin lokaci ba kamar yadda yake iƙirari."

"Da fari ban yi niyyar halartar zaman da Chief Ayo Adebanjo ya faɗa mini ba."

"Amma sai na canja shawara saboda na karrama Chief Adebanjo a matsayinsa na dattijon Bayarbe da nake mutuntuwa sosai.

"Shi Obasanjo a maganarsa ya ce duk mai son yin sulhu da shi sai dai ya je gidansa na Abeokuta."

"Bana buƙatar yin zaman sulhu da shi ko kaɗan."

"An rufe wannan babi, ba zan ma iya zuwa gidansa ba"

A baya Legit.ng Hausa ta wallafa labarin cewa babban hafsan rundunar soji, Janar Tukur Buratai, ya gargadi manyan sojoji a kan juyin mulki.

Buratai ya ce dimokradiyya ta zo kenan, zama daram, a saboda haka lokacin katsalandan daga wurin sojoji ya wuce.

Buratai ya bayyana hakan ne yayin da ya ke gabatar da jawabi bayan ya kammala daura damarar kara girma ga sabbin manyan sojoji 39 da aka karawa girma zuwa mukamin manjo janar.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel