Zamfara: Ma'aikatan INEC da suka bace yayin zaben maye gurbi sun bayyana

Zamfara: Ma'aikatan INEC da suka bace yayin zaben maye gurbi sun bayyana

- A Ranar Asabar, 6 ga watan Disamba, INEC ta gudanar da sauran zabukan maye gurbi a fadin Nigeria

- Zamfara da Bauchi da Legas na daga cikin jihohin da zaben mayen gurbi ya shafa kuma aka fafata tsakanin APC da PDP

- Sai dai, baturen zabe a jihar Zamfara, Farfesa Ibrahim Magawata, ya ce an soke zaben mazabu biyar a karamar hukumar Bakura

Ma'aikatan wucin gadi guda biyu da suka bace yayin zaben maye gurbi na ranar Asabar a jihar Zamfara sun bayyana, TheCable ta rawaito ranar Litinin.

An samu matsalar satar akwatin zabe da barkewar rikici a mazabar 001 da ke karamar hukumar Bakura yayin zaben maye gurbin.

Yayin da take gabatar da sakamakon mazabar, wakiliyar INEC mai kula da mazabar, A'isha Bawa, ta ce ta nemi ma'aikatan Sama ko kasa, ba ta gansu ba, sun bace bat bayan barkewar rikici.

KARANTA: A villa ake iskanci na gaske kuma Buhari ne jagora; Aisha ta mayar da martani a kan gargadin shugaba Buhari

Da ya ke magana da manema labarai ranar Litinin, Nick Dazang, darektan sashen wayar da kan ma su zabe da yada labarai a INEC, ya ce an samu ma'aikatan cikin koshin lafiya.

Zamfara: Ma'aikatan INEC da suka bace yayin zaben maye gurbi sun bayyana
Zamfara: Ma'aikatan INEC da suka bace yayin zaben maye gurbi sun bayyana @Thecable
Source: Twitter

"Ina Mai farin cikin sanar da cewa an samu ma'aikatanmu na wucin gadi da su ka bata, an samesu cikin koshin lafiya, kamar yadda sakataren INEC a jihar Zamfara, Garba Lawal, ya tabbatar min.

KARANTA: An kama Idris mai wankin mota a hanyarsa ta zuwa ya siyar da galleliyar motar kwastoma

"Hedikwatar INEC ta na mika sakon godiya ga Garba da jami'an tsaro da suka hana idonsu bacci wajen neman ma'aikatan tare da tabbatar da cewa an samesu cikin koshin lafiya," a cewar Dazang.

Dazang ya bayyana cewa ma'aikatan sun gudu ne domin tsira da rayuwarsu, amma sai suka yi batan hanya, su ka kasa gane hanyarsu ta dawowa.

A baya Legit.ng Hausa ta wallafa labarin cewa babban hafsan rundunar soji, Janar Tukur Buratai, ya gargadi anyan sojoji a kan juyin mulki.

Buratai ya ce dimokradiyya ta zo kenan, zama daram, a saboda haka lokacin katsalandan daga wurin sojoji ya wuce.

Buratai ya bayyana hakan ne ranar Juma'a yayin da ya ke gabatar da jawabi bayan ya kammala daura damarar kara girma ga sabbin manyan sojoji 39 da aka karawa girma zuwa mukamin manjo janar.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel