ISWAP ta kashe sojoji 10 tare da yin garkuwa da guda ɗaya a jihar Borno

ISWAP ta kashe sojoji 10 tare da yin garkuwa da guda ɗaya a jihar Borno

- Jaridar Vanguard ta rawaito cewa mayakan kungiyar ta'addanci ta ISWAP sun hallaka dakarun rundunar sojoji 10

- An yi musayar wuta mai zafin gaske a yayin da sojoji suka yi wa sansanin ISWAP kawanya a Alagarmo da ke Damboa

- Gwamnan Borno, Farfesa Umar Zulum, ya ce duk da kashe-kashen da ake yi, an fi samun zaman lafiya a jihar a karkashin mulkin Buhari

Mayakan kungiyar ta'addanci ta ISWAP, wacce ke haɗe da ƴan jihadin ƙungiyar IS a jihar Borno, sun sheƙe sojoji goma tare da yin garkuwa da ɗaya daga cikinsu, kamar yadda majiyoyi biyu daga jami'an tsaro suka bayyanawa Vanguard.

An yi ɓarin wutar ne a ranar Litinin lokacin da tawagar sojoji suka yiwa sansanin ISWAP ƙawanya a ƙauyen Alagamo dake garin Damboa.

"Mun rasa sojoji goma (10) a gumurzun, sannan ƴan ta'addar sun yi garkuwa da ɗaya," kamar yadda wata majiya daga ɓangaren tsaro ta shaidawa AFP a ranar Talata.

KARANTA: Gwamnatin tarayya ta na amfani fasahar Isra'ila wajen leken asirin wayoyin 'yan Nigeria

"Sun ɗauki jami'in da suka yi garkuwa da shi ne lokacin da alburushin sojoji ya ƙare aka cimmu su", a cewar majiyar.

ISWAP ta kashe sojoji 10 tare da yin garkuwa da guda ɗaya a jihar Borno
ISWAP ta kashe sojoji 10 tare da yin garkuwa da guda ɗaya a jihar Borno @Vanguard
Source: Twitter

"An yi gumurzu mai zafi a tsanani, kuma suma ƴan ta'addan sun rasa mutanensu da dama, amma duk da haka sun kerewa sojojin," kamar yadda majiyarmu ta biyu ta tabbatar da adadin mutanen da su ka mutu.

KARANTA: A villa ake iskanci na gaske kuma Buhari ne jagora; Aisha ta mayar da martani a kan gargadin shugaba Buhari

Ƴan ta'addan sun ƙwaci ababen hawa huɗu,wanda suka haɗar da Babbar motar ɗaukar kaya da kuma motar yaƙi, kamar yadda majiyar Vanguard ta biyu ta shaida mata.

Dukkan majiyoyin sun nemi a sakaye sunansu.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa gwamna Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce tsaro ya karu a jihar Borno da arewa ma so gabas a karkashin mulkin Buhari duk da cigaba da kashe-kashen da mayakan Boko Haram ke yi.

A cewar gwamnan, shaidu a kasa sun nuna cewa al'amuran harkokin rayuwa sun fara dawowa a kananan hukumomin da jama'a suka kauracewa a baya, kafin mulkin Buhari.

Farfesa Zulum ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin kungiyar dattijan arewa a karkashin jagorancin shugabanta, Ambasada Shehu Malami, da kuma sakatarenta, Audu Ogbeh.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel