Yanzu-yanzu: Dan majalisa, Hernan Hembe, ya sauya sheka jam'iyyar APC

Yanzu-yanzu: Dan majalisa, Hernan Hembe, ya sauya sheka jam'iyyar APC

- Jam'iyyar APC ta samu karuwa a majalisar wakilan tarayya

- Tsohon dan cikinta, Herman Hembe, ta koma bayan nisan kiwon da yayi

- Tuni dai shugaban kwamitin rikon kwaryan APC, Mai Mala Buni yace PDP zata tsorata da irin mutanen da zasu koma jam'iyyar

Dan majalisar wakilan tarayya, Herman Hembe, mai wakiltar mazabar Vandeikya/Konshisha ta jihar Benue, ya sauya sheka daga jam'iyyar All Progressives Granda Alliance APGA, zuwa jam'iyyar All Progressives Congress APC.

Majalisar wakilai ta bayyana hakan a shafinta na Tuwita ranar Talata, 8 ga Disamba, 2020.

Herman Hembe ya kasance dan APC a baya kafin kotu ta tunbukeshi daga kujerar majalisa ta mikawa abokin hamayyarsa, Dorathy Mato a shekarar 2017.

Bayan haka ya koma jam'iyyar APGA inda ya sake takara a zaben 2019 kuma yayi nasara.

Hembe ya shiga sahun yan majalisan da suka koma jam'iyyar APC kwanakin nan.

KU KARANTA: 2023: Jam'iyyar APC ta sahalewa Umahi, Dogara da wasu tsayawa takara

Yanzu-yanzu: Dan majalisa, Hernan Hembe, ya sauya sheka jam'iyyar APC
Yanzu-yanzu: Dan majalisa, Hernan Hembe, ya sauya sheka jam'iyyar APC
Asali: UGC

A makon karshe na watan Nuwamba, Sanata mai wakiltar Adamawa ta Arewa, Elisha Ishaku Abbo, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Ishaku Elisha Abbo, ya bayyana cewa ya sauya daga jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) domin yayi takara a zaben gwamnan 2023.

Hakazalika a jiya, Sanata Nyako ya sauya sheka daga jam'iyyar African Democratic Congress ADC zuwa APC.

KU DUBA: Yanzu-yanzu: Zan bude boda nan ba da dadewa ba, Buhari

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng