Rashin Tsaro: Wani mutumin Katsina ya canza sunansa daga Buhari

Rashin Tsaro: Wani mutumin Katsina ya canza sunansa daga Buhari

Wani mutum mai matsakaicin shekaru, mazaunin Damari a karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina, Lawal Na Buhari, ya yi Alla-wadai da tabarbarewan tsaro a jihar.

Saboda haka, ya sauya sunansa daga Lawal Na Buhari zuwa Lawal na Manzon Allah.

Lawal, ya baiwa al'ummar garin mamaki yayinda ya manna fostocin sauya sunansa a garin, saboda nuna bacin ransa kan rashin tsaro.

Lawal ya ce gwamnatin tarayya karkashin shugaba Muhammadu Buhari ta yi kasa a gwiwa wajen magance matsalar tsaro a fadin tarayya musamman jihar Katsina.

A rahoton da Kastina Post ta wallafa, Lawal Idi, wanda ya shahara da Lawal Na Buhari, saboda soyayyar da yake yiwa Buhari, amma yanzu ya dawo rakiyar shugaban kasan.

"Ya wallafa fostoci dauke da hotonsa da sanarwan, wanda ya manna a wurare daban-daban," Jaridar ta wallafa.

"Akan Fostocin, Lawal ya rubuta cewa duk wanda ya cigaba da kiransa 'Na Buhari' zai fuskanci fushinsa."

Damari na daga cikin garuruwa a karamar hukumar Sabuwa dake fuskantar matsalar tsaro da hare-haren yan bindiga.

Lawal Dan Idi yace: " Assalamu Alaikumu Warahmatullahi wabarakatuhu. Ni Lawal Dan Idi Damari, Ina sanar da al'umma masoya Manzon Allah (SAW) cewa kada wanda ya kara kira na da suna Lawal Na Buhari."

"Maimakon haka inaso a rika kira na da suna Lawan Na manzon Allah."

"Idan kuma mutum bai bari ba, duk matakin da na dauka akanshi, shi ya jawo ma kansa."

KU KARANTA: An sauke dukkan shugabannin jam'iyyar APC a fadin tarayya

Rashin Tsaro: Wani mutumin Katsina ya canza sunansa daga Buhari
Rashin Tsaro: Wani mutumin Katsina ya canza sunansa daga Buhari Credit: Katsina Post
Asali: UGC

KU DUBA: Dan majalisa, Hernan Hembe, ya sauya sheka jam'iyyar APC

A wani labarin kuwa, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba zai bude iyakokin Najeriya.

Ya bayyana hakan ga gwamnonin Najeriya 36 a ganawar da yayi da su ranar Talata, 8 ga watan Disamba, 2020.

Buhari ya ce ya rufe iyakokin ne domin hana fasa kwabrin makamai da kwayoyi amma tun da yanzu makwabtan Najeriya sun hankalta, zai iya bude wa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng