Tura ta kai bango: Mutanen gari sun kashe dan bindiga da duka a Katsina

Tura ta kai bango: Mutanen gari sun kashe dan bindiga da duka a Katsina

- Fusattaun matasa a karamar hukumar Malumfashi da ke jihar Katsina sun yi wa dan bindiga dukan da ya zama ajalin sa

- Dan bindigar ya gamu da ajalinsa bayan da suka kai hari su uku gidan wani mutum, Hari Bello kuma ya yi kururuwa mutane suka biyo su kuma suka kama shi

- Jami'an yan sanda sun rankaya da shi asibiti tare da yaran da suka jikkata a gidan da suka kai harin, sai dai shi ya mutu a asibitin sakamakon mugun dukan da ya sha

Yan sandan Jihar Katsina a ranar Asabar sun tabbatar da mutuwar wani da ake zargi dan bindiga ne a karamar hukumar Malumfashi da ke jihar.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Gambo Isah, ya ce yan bindiga kusan guda uku, da misalin 1:30 na daren Asabar, sun kai hari gidan wani mutum, Hari Bello, sun kuma jikkata yara biyu.

Mutanen gari sun kashe dan bindiga da suka a Katsina
lMutanen gari sun kashe dan bindiga da suka a Katsina. Hoto daga @PremiumTimesNG
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hisbah ta yi bincike ɗaki-ɗaki don kama masu baɗala a Kano (Hotuna)

Jami'an sun ce wanda aka kaiwa harin sun yi kuwwa, wanda hakan ya ja hankalin makwabta da yan sanda. Saboda haka an kora yan bindigar kuma an ci gaba da bin su. An tarar da daya daga cikin yan bindigar kuma fusatattun mutanen suka rufe da duka.

KU KARANTA: A rataye ni a tsakiyar kasuwa har in mutu, in ji wanda ake zargi da garkuwa a Kano

Malam Isah ya kara da cewa yan sanda sun debi wanda aka kaiwa harin da dan bindigar zuwa babban asibitin Malumfashi don duba lafiyarsu. An yi wa musu magani kuma an sallame su sai dai dan bindigar da ya mutu a asibitin.

Premium Times ta ruwaito cewa 'yan sanda na ci gaba da binciken wanda suke laifin da duba yiwuwar kama su tare da gurfanar da su.

A wani labarin daban, kungiyar gwamnonin Arewa maso gabas, NEFG, ta koka kan abinda ta kira rashin adalci da gwamnatin tarayya ke mata a bangaren gine-ginen tituna a yankin ta.

Kungiyar wadda ta hada da gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno Gombe, Taraba da Yobe ta bayyana hakan ne a ranar Juma'a cikin sakon bayan taro mai dauke da sa hannun shugabanta, Gwamna Babagana Zulum a karshen taronta na 3 da aka yi a Yola babban birnin Jihar Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164