Gwamnatin jihar Kaduna ta rushe gidaje 50 a kusa da cibiyar Idanu
- Gwamnatin jihar Kaduna a ranar Litinin ta rushe wasu gidaje guda 50 da ke hurumin cibiyar ido ta kasa
- A cewar gwamnatin jihar, jama'a sun mallaki filaye tare da yin gini a filayen cibiyar ta haramtacciyar hanya
- Barrister Ryndeen John, wanda ya wakilci cibiyar idanu, ya ce gwamnatin tarayya ta biya diyya ga waɗanda rusau din ya shafa
Hukumar kula da tsara birane ta jihar Kaduna, KASUPDA, ta rushe gidaje 50 da ke hurumin cibiyar ido ta ƙasa a garin Kaduna, kamar yadda Daily Nigerian ta rawaito.
Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar KASUPDA, Nuhu Garba,shine ya sanar da hakan yayin zantawa da Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) a ranar Litinin a Kaduna.
Acewarsa, an fara gudanar da rusau bisa umarnin da kotu ta baiwa hukumar damar cire dukkan gine-ginen da suka saɓawa doka a filin da ya ke mallakin cibiyar idon.
KARANTA: A Villa ake iskanci na gaske kuma Buhari ne jagora; Aisha ta mayar da martani akan gargadin Buhari
Ya ce rusau din ya zo ne bayan rikicin ƙasa da ake ta yi a kotu wanda aka ɗauki tsawon shekara 20 ana shari'ar a babbar kotun jihar Kaduna akan wanda ke da haƙƙin mallakar filin cibiyar ido ta ƙasa.
Ya ce Kotun ta yi umarni ga wanda suka ƙetare iyakar ƙasa da su tashi ko kuma a tashe su ta ƙarfi, wanda hakan ya yi sanadiyyar rushe gidajen da ke wurin.
Malam Garba ya ce hukumar za ta cigaba da tabbatar da an bi hanyar da doka ta tanada wajen siye da siyar da kadarorin da suka shafi ƙasa a jihar.
KARANTA: An kama Idris mai wankin mota a hanyarsa ta zuwa ya siyar da galleliyar motar kwastoma
"Sama da shekaru kenan muna sanarwar jan kunne da gargaɗar jama'a kan kada su siya, ko su siyar, ko su saka kansu cikin dukkan wata hada-hada ko cinikayyar mallakar ƙasa a filin da yake mallakin cibiyar ido ta kasa amma sai suka yi burus da kiran namu," a cewarsa.
KASUPDA tayi gargaɗin cewa duk wanda ya sayi ƙasa a filayen gwamnati za'a hukunta shi yadda doka ta tanada.
Barrister Ryndeen John, wanda ya wakilci cibiyar idanu, ya ce gwamnatin tarayya ta biya diyya ga waɗanda rusau din ya shafa.
A baya Legit.ng ta rawaito cewa gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da cewa ta fara tantance matasan da za'a dauka aiki a matsayin 'yan sandan jiha.
Sanatan Kaduna ta tsakiya, Uba Sani, ya ce ya na aiki a kan wani kudiri da zai samar da dokar kirkirar 'yan sandan jihohi daban da na tarayya.
Kwamishinan kananan hukumomi a jihar Kaduna, Ja'afaru Sani, ya ce tantance matasan shine mataki na farko a yunkurin samar da yan sanda jihar.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng